Rikicin Filato: "GWAMNATIN TINUBU TA GAZA A KAN HARKOKIN TSARO" - Dokta MB Lamido
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Dan takarar shugaban kasa a 2027, kuma mai taimakon jama’a, Dokta Mohammed Bashir Lamido, ya bayyana matukar damuwa dangane da tashe-tashen hankula na kabilanci da na addini a jihar Filato.
"Rashin magance musabbabin wadannan fadace-fadacen da gwamnatocin tarayya da na Jihohi suka yi sama da shekaru ashirin ya sa al'ummomi cikin rudani".
Dokta MB Lamido ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ambasada Abdullahi Isah, ya rabawa manema labarai a Abuja. A cewar sanarwar, Dokta Bashir Lamido ya lura cewa hare-haren baya bayan nan a Bokkos na tunatar da mu yadda gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta kasa samar da isasshen tsaro ga ‘yan Najeriya. Hare-haren da ake kai wa al’ummar Hausa Fulani, musamman a Jos ta Kudu, da Bukur, da Barikin Ladi, da sauran yankuna, ba za a amince da su ba.
“Na ji takaicin yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta dauki isassun matakan tabbatar da tsaro da jin dadin wadannan ‘yan kasa ba,” inji shi.
A matsayinsa na dan siyasa mai kishin kasa kuma shugaban ‘yan kasuwa, Dokta Bashir Lamido ya yi alkawarin tallafa wa wadanda wannan rikice-rikicen kabilanci ya rutsa da su tare da taimakon jin kai da sauran tallafi don rage musu radadi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da na Jihohi da su gaggauta daukar matakin magance musabbabin tashe tashen hankula a Filato da sauran Jihohin kasar nan. Dokta Lamido ya bukaci ‘yan Najeriya masu kishi da su hada kai da shi wajen tallafa wa wadanda rikicin kabilanci ya shafa.
Dokta Bashir Lamido ya roki ‘yan Najeriya da su yi la’akari da zabin shugabanci na gari a 2027, domin samun gwamnatin da zata magance wadannan batutuwa yadda ya kamata. Ya kuma bayar da shawarar a fitar da jam’iyyun APC da PDP domin samar da sabon shugabanci da ceto Najeriya daga halin da take ciki a zabe mai zuwa na 2027.