MATASAN DA SUKA YI TATTAKI DAGA KATSINA SUN ISA ABUJA LAFIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Wasu matasa biyu da suka tashi daga garin Malunfashi don yin tattaki a ƙasa zuwa Abuja sun isa yau Litinin 28 ga Afirilu, 2025 cikin ƙoshin lafiya. Matasan Abubakar Aliyu (Ɗan Habu) da Muhammadu Ibrahim (Abba) sun fara yin wannan tattakin tun daga 18 ga Afirilu, 2025 don zuwa Abujan bisa ga manufa da kuma ƙudurin ganin wasu muhimman mutane huɗu a babban birnin tarayyar. Mutun na farko da matasan ke fatan kaiwa wannan ziyara shi ne, Mai baiwa Shugaba Ahmed Bola Tunubu shawara akan harkokin siyasa Alhaji Ibrahim Kabir Masari. "Muna so mu nunawa duniya irin yadda wannan bawan Allah yake taimakawa don kawo ci gaban jahar shi da ƙasa baki ɗaya domin ganin siyasar da ake yi a ƙasa ta cigaba da zama da sosai saɓanin yadda wasu ke ganin salon mulkin na demukaraɗiyar da ake yi.
Kazalika, mutun ne wanda ya kula da rayuwar matasa don ganin sun dogara da kansu".
Sauran mutanen da matasan suka yi tattakin don ganin su harda matar Mataimakin Shugaban ƙasa Hajiya Nana Kashin Shetima. Muhammadu Ibrahim ya shaidawa wannan kafa ta wayar salula cewar, yana da wani saƙo na musamman wanda ya samu acikin wani mafarki da yayi da yake son shaidawa uwargidan kai tsaye. Har'ila yau, akwai Ministan harkokin mata Hajiya Imaam Suleiman Ibrahim domin yaba mata akan irin yadda take tafiyar da harkokin ta da kuma irin yadda take ta ƙoƙarin ta kawo mata harkokin ci gaba.
Mutun na ƙarshe da matasan ke fatan kaiwa ziyara shi ne, Babban Sufeton 'Yansanda na ƙasa Mista Kayode Ebekuta, wanda suka ce, jami'in tsaro ne wanda ya jajirce a bisa aikin shi da kuma irin yadda yake sa ido akan batun harkokin tsaro.
Sai dai, ga dukkan tafiyar da abubuwa na yau da kullum ba za a rasa samun 'yan matsalolin nan da can ba. Kasancewar irin yadda ake fuskantar matsalar tsaro musamman a arewacin ƙasar, masu tattakin sun fuskanci wasu matsaloli a bisa hanya musamman a lokacin kwanciya barci in yayi.
Wasu lokuttan kamar yadda suka ce, suna kwana kodai a masallaci ko cikin almajirai a inda suka samu hakan. Sannan sukan fuskantar jami'an tsaro wanda sai sunyi cikakken bayani tare da nuna katin su na shaidar ƙungiyar agaji. A haka dai suka ci gaba da tafiyar har zuwa wannan rana da suka samu isa cikin Abuja.