ƘUNGIYAR 'YAN JARIDU NUJ TA JIHAR KATSINA TA MIƘA TA'AZIYYAR RASUWAR MAHAIFIYAR GWAMNA RAƊƊA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ reshen jahar Katsina ƙarƙashin shugabancin Kwamared Tukur Hassan Ɗan-Ali ta nuna alhinin rasuwar Hajiya Safara'u mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina Mal. Dikko Ummaru Raɗɗa .
Kamar yadda shugaban ya ce, "Rasuwar Hajiya Safara'u babban rashi ne ba ga iyali kaɗai ba, har ga ɗaukacin mazauna jihar Katsina baki ɗaya.
"Duba da irin gudunmawar da ta bayar wajen ci gaban jiharmu ta kasance abin tunawa a yanzu da nan gaba. Yayin da muke miƙa ta’aziyyarmu a madadin ɗaukacin ‘yan jaridu masu aiki a Jihar Katsina, muna kuma yin addu’ar Allah ya jiƙanta da Aljannatul Firdausi.
Har'ila yau, shugaban ya bukaci ɗaukacin ‘yan jaridun masu aiki a Jihar Katsina da su sanya marigayiya Hajiya Safara’u Ummaru Raɗɗa a cikin addu’o’insu musamman a wannan wata na Ramadan.