ƘUNGIYAR MASU SAYAR DA DANKALIN TURAWA NA MIƘA TA'AZIYYAR RASUWAR MAHAIFIYAR GWAMNA RAƊƊA

ƘUNGIYAR MASU SAYAR DA DANKALIN TURAWA NA MIƘA TA'AZIYYAR RASUWAR MAHAIFIYAR GWAMNA RAƊƊA

Ƙungiyar masu sayar da Dankalin turawa ta jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Alhaj Abu Bros na miƙa saƙon ta'aziyyar ta ga Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda PhD bisa rasuwar mahaifiyar shi Hajiya Safara'u Umar Barebari.
"wannan rashin ba na Gwamna da iyalan shi kaɗai ta shafa ba, ta shafi al'ummar jahar baki ɗaya kasancewarta uwa ta gari wadda ta bayar da kyakkyawar tarbiya, rikon amana da kuma sanin darajar mutane ga 'ya'yanta."Ni da 'yan ƙungiya muna alhinin rashin wannan dattijuwa tare da roƙon Allah ya gafarta mata".
Kazalika, ƙungiyar ta miƙa saƙon ta'aziyyar ga Maimartaba sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir bisa ga rashin wannan 'yar-uwa ta shi mahaifiya ga Gwamna Radda. Kazalika, ƙungiyar ta miƙa wannan ta'aziyyar ga ɗaukacin al'ummar jahar Katsina baki ɗaya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post