Umra2025: AN SANAR DA LOKACIN ZIYARAR RAWDAH AL-SHARIF A KWANAKI 10 NA ƘARSHEN RAMADAN
A cewar Hukumar Kula da Masallacin Harami da Masallacin Annabi, an sanya sa'o'in ziyarar mata daga karfe 6:00 na safe zuwa 11:00 na rana
Hukumar dake Kula da Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun sanar da sa'o'in ziyarar Rawdah Al-Sharif a Masallacin Annabi da ke Madina a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan.
A cewar hukumar, an sanya sa'o'in ziyarar mata daga karfe 6:00 na safe zuwa 11:00 na safe, maza za su iya zuwa daga karfe 11:20 na safe zuwa 8:00 na dare, tare da karin lokacin daga karfe 11:00 na dare zuwa 12:00 na cikin wannan dare da kuma daga 2:00 na cikin wannan zuwa 5:00 na asuba
Hukumar ta jaddada kudirinta na shiryawa da kuma gudanar da ziyarar zuwa Rawdah Al-Sharif, ta yadda za a tabbatar da samun walwala ga masu ibada. Masu ziyara dole ne su rubuta lokuttan da zasu shiga domin yin addu'o'in su ta hanyar manhajar Nusuk