Katsina: BABBAN JOJI YA SALLAMI 4 YA BAYAR DA BELIN FURSUNONI 91 DAGA GIDAN GYARAN HALI

Katsina: BABBAN JOJI YA SALLAMI 4 YA BAYAR DA BELIN FURSUNONI 91 DAGA GIDAN GYARAN HALI
 Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 Babban Jojin Jahar Katsina Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya ba da belin fursunoni 91 sannan aka sallame 4 daga gidan gyaran hali a ranar Alhamis. 20 ga Maris, 2025 a matsayin wani É“angare na Æ™oÆ™arin rage cunkoson cibiyoyin gyaran hali a jihar. Babban Joji ya ba da umarnin bayar da belinsu tare kuma da sallamar a lokacin atisayen duba gidajen gyaran halin na shekara ta 2025 wanda aka gudanar a tsohuwar cibiyar gyaran halin ta Unguwar Yari Katsina. Da yake jawabi a yayin atisayen, Babban Jojin ya bayyana cewa karamin kwamitin dake kula da wannan sashe ya ba da shawarar cewa a rage cunkoson cibiyoyin gyara halin saboda dalilai daban-daban. An saki wasu daga cikin fursunonin da suka dawo cikin ’yanci saboda shekaru, ko dadewa a tsare tare da yanayin lafiya. Babban Jojin ya bayyana cewa daga yanzu, za a rubuta cikakkun bayanai da hotunan fursunonin da aka saki don ajiyewa saboda gaba. Mai Shari'ar Danladi ya bukaci fursunonin da aka saki da su zama 'yan kasa masu bin doka da oda, yana mai gargadin cewa ba za su iya samun irin wannan damar ba idan aka sake samun su da wasu laifuka.
 A nasa bangaren, Kwanturola mai kula da gidan gyaran halin na jihar Katsina, CC Umar Baba, ya yaba da kokarin da Babban Jojin ya yi, inda ya bayyana cewa atisayen ya amfanar da cibiyoyin gyaran hakin a jihar. "Irin waÉ—annan ayyukan na taimakawa wajen kula da fursunoni ra rage tashin hankali a cikin cibiyoyin gami da inganta aiyukan gyaran halin," in ji CC Umar. Akan haka, Babban jami'in mai kula da jahar Katsina CC Baba ya yi kira zuwa ga alkalai da su yi amfani da matakan da ba na tsarewa ba don rage cunkoso a wuraren gyaran halin domin samun damar gudanar da ayyukansu na gyarawa da tarbiyantar fursunonin domin sake maido da matsayin su na 'yan kasa masu bin doka, a cewar sanarwar da aka rabawa manema labarai wadda jami'in hulda da jama'a na jihar ASC Najib Idris Kunduru ya sanya wa hannu.

Post a Comment

Previous Post Next Post