Da xumi xumi. ALLAH YA YIWA MAHAIFIYAR GWAMNA RAXXA RASUWA A YAU

Da xumi xumi. ALLAH YA YIWA MAHAIFIYAR GWAMNA RAXXA RASUWA A YAU 

 Daga Ahmed Kabir S/Kuka,
 Katsina. A safiyar yau lahadi aka tashi da alhinin rashin mahaifiyar Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Raxxa Hajiya Safara'u Umar Barebari a garin Raxxa bayan ta sha fama da rashin lafiya. Sanarwar mutuwar dattijuwar ta fito daga wajen Mataimakin Gwamnan Jahar Malam Faruk Jove. Hajiya Safara'u mai kimanin shekaru 93 ta rasu ta bar  'ya'ya maza da mata gami da jikoki. Daga cikin 'ya'yan da ta bari akwai shi kan shi Maigirma Gwamna Malam Dikko Umar Radda, sai Maigarin Raxxa Alhaji Kabir da Mani tare da Hajiya Hauwa Umar Raxxa da sauran 'yan uwan shi. Za' a yi janazar ta a can garin Raxxa a yammancin yau. A halin yanzu dai shi Maigirma Gwamna Raxxa yana qasar Saudiya yana aikin Umra.

Post a Comment

Previous Post Next Post