YADDA AKA KADDAMAR DA YAƘIN NEMAN ZAƁE A ƘARAMAR HUKUMAR KAITA A CIKIN HOTUNA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar Talatar nan 4 ga watan Fabrairu, 2025 jam'iyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban karamar hukumar Kaita Injiniya Bello Lawal Yandaki a garin Abdallawa dake cikin karamar hukumar ta Kaita.
Dan majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar ta Kaita Honarabil Kwaskwaro a wajen bikin kaddamar da yakin neman zaben. A bayan shi daga Alhaji Nasiru Tarkama ne mai jiran kujerar karamar hukumar ta Kaita.
Kwamishinan ƙasa da tsare tsare na Jahar Katsina Dokta Faisal Kaita yana jawabi a wajen bikin kaddamarwar, a garin na Abdallawa.
Wani sashe na dandazon mutanen da suka halarci wannan bikin kaddamarwar da suka fito daga mazabun dake cikin karamar hukumar ta Kaita.
Mataimakin shugaban jam'iyar ta APC na jaha Alhaji Bala Abu Musawa na daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan biki. Akwai Babban Daraktan hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Yunusa Dankama, da shugaban karamar hukumar Jibiya Alhaji Maitan, shugaban matasa kuma Garkuwan Kaita Alhaji Isma'ila Yandaki tare da sauran manyan baki daga ciki da kuma wajen Karamar hukumar masoya.
Anyi taron cikin kwanciyar hankali da kuma daukar matakan tsaro