WA NE NE MUSA GAFAI? - Nazari

WA NE NE MUSA GAFAI? - Nazari

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Mafi yawan abin da kan faɗowa mutane a rai idan aka yi tambayar 'Wa ne ne wane' shi ne, za'a fara bayar labarin tun lokacin haihuwa, ilmi da sauran su na wanda aka yi tambayar akan shi. To a wannan nazari ba mu tabo batun ranar haihuwa ko karatu da sauran su ba, sai dai kawai sunan unguwar da ta tabbatar da wanda zamu yi magana akan shi.
Mun kalli dalilan da kan sa har ayi tambaya akan sanin mutum saboda wasu abubuwa da yayi acikin al'umma wanda hakan kan sa yayi fice.
Alhaji(Dr) Musa Yusuf Gafai wani matashi ne daga cikin matasan jahar Katsina wanda ya kawo wasu abubuwan da har yanzu muna cikin laluben ko za a samu wanda zai biyo bayan shi. Bayan 'yan karance-karancen da yayi, Allah ya sa matashi ne mai son ganin ci gaban matasa da sauran al' umma musamman ta fuskar dogaro da kai, taimakon jin ƙai, cuɗanya da kuma ƙoƙarin kawo abin da zai haɗa kai. Ɗan abin da zamu fara kawowa acikin wannan nazari da muka yi shi ne, ƙoƙarin haɗan masu sana'ar saye da sayar da wayar salula, inda ya kafa wata ƙungiya mai suna KAGASA. Wannan ƙungiya ta haifar da 'ya'yaye masu ido domin baya ga haɗa kan masu gudanar da sana'ar an kuma tsabtace ta daga hannun ɓata gari. Ƙungiyar KAGASA bisa jagorancin shi babu inda bata je ba domin tallata da kuma baiyana Manufofi da fa' idojin dake kan haɗa kai.
Likkafa na yiwa Alhaji Musa Gafai gaba bisa ga wancan kyakkyawan ƙuduri na shi gami da samun addu'o'i da sa albarkar mahaifa, sai Gafai ya ci gaba da haɓaka ita wannan sana'a ta sayar da wayar salula tare da sauran kayan ta. Har ila yau, bai tsaya a tuwo na mai na ba, a'a, sai ya cigaba da nemo matasa yana koyar da su wannan sana'a tare kuma da buɗe rassa domin a samu abin yi. Wannan tagomashi da ya rika samu a tsakanin jama'a, sai kuma tunanin tallafawa marassa ƙarfi shigo a zuciyar shi. Musa Gafai ya riƙa sayen kayan abinci yana baiwa bayin Allah wasu lokuttan har abin rufe fatar jiki. Kuma dukkan kuɗaɗen da yake kashewa har zuwa wannan rubutu bamu ji inda aka ce wani ko wasu sun kawo wani tallafi don gudanar da wancan aiki da yake yi. Musa Gafai ya ƙara faɗaɗa tallafin shi ta fuskar bunƙasa ilmi na addini da na boko. 'Yan unguwar Gafai da kewaye shaida ne akan hakan, hatta da ita kanta makarantar ta Gafai inda nan ne ya fara samun ilmin zamani.
Alhaji Musa Gafai, ya zamo inwa ce wadda ake cewa baki ƙyamar kowa, domin ya zamo kowa na shi ne. In ba ance maka ga shi ba, tabbatar a yadda kake jin labarin shi abin zai baka mamaki. Ba wai wannan rubutu ko nazari yana kururuta shi ba, a'a, zahirin abin da ke faruwa ne daga wajen shi.
SIYASA Baya ga siyasar kafa ƙungiya, Alhaji Musa Gafai ya shigo harkokin siyasa da ƙafar dama. Siyasar 2023 wadda ta shigo da abubuwa iri-iri, sai ga shi yana daga cikin matasan da suka yi tasiri a siyasar jahar Katsina da ma ta ƙasa baki ɗaya. Shi matashin ɗan siyasar da ya kawo babba daga cikin manyan 'yan takarar shugabancin ƙasar nan. Alhaji Musa Gafai ne ya kawo Rochas a jahar Katsina a matsayin ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a jam' iyar APC a wannan zabe na 2023 kuma gwarjinin shi yasa dukkan ƙananan hukumomin jahar Katsina babu inda babu ofishin wannan ɗan takara. Wani abin ban sha'awa, waccan harka ta siyasa bata sa ya bar waccan hidimar jama'ar da aka san shi da ita, sannan bai bar kasuwancin na sayar da wayar salula ba, hasali ma, sai ya zamo ɗaya daga cikin masu kafa na'urorin tsaro a ofisoshin gwamnati.
Wannan siyasa ta Rochas ta ƙara fito da baiyana ko wa ne ne Musa Gafai, domin sai da ya zamo tamkar wutar daji acikin ɗan karamin lokaci. Ganin hakan, ya ba Alhaji Musa Gafai ƙwarin gwuiwar fitowa ta kara tare da taimakon shawarar wasu daga cikin abokai da masoya, inda ya fito takarar kujerar Ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga shiyyar Katsina. Har ila yau, Alhaji Musa Gafai shi ne wanda ya assasa sashen yaƙin neman zaɓen Gwamna mai ci yanzu Malam Umar Dikko Radda PhD CON. Shi ne ya kawo wannan take na KATSINA TA DIKKO ce. Amma da yake bayar da mulki daga Allah ne, sai yasa baiyi nasara akan wancan takara da ya shiga ba. To hakan yasa ya fita daga harkokin siyasa baki ɗaya?
TAFIYAR SHI ZUWA ƘARIN NEMAN ILMIN SIYASA Kamar yadda masu iya magana kance, komin kake da kyau, to ka ƙara da wanka, kuma ita siyasa bata da aboki ko makiyi na har abada ba. Alhaji Musa Gafai yayi tattaki inda ya koma jam'iyar adawa ta PDP. To sai dai mafi yawan mutane sun ɗauka cewar ɓacin rai yasa yayi canjin sheƙar jam'iyar siyasa, to amma bisa ga bincike da nazarin da wannan kafa ta ASKGLOC NEWS ta yi akan wancan batun, ta gano cewar ashe matashin ya tafi ƙarin neman ilmi ne a fuskar siyasa. Ya shiga PDP kuma ya bayar da gudunmuwa fiye da yadda ake tunani. Shigar ta shi a PDP bai sa ya rabu da mutanen shi na APC ba domin yasan dalilan da suka sa ya koma ita waccan jam'iya.
BAYAN KARATU YA DAWO GIDA Bayan kammala wancan karatu na siyasa a ita jam'iyar adawar ta PDP Alhaji Musa Gafai ya dawo gida ko ajiye batun siyasar yayi baki ɗaya? Abin da rubutun wannan nazari zai yi tsokaci kenan a nan gaba kaɗan. 

Post a Comment

Previous Post Next Post