Hajji 2025: GWAMNA RAƊƊA ZAI JAGORANCI TATTAUNAWA DA SAURAN GWAMNONI DON SAMARWA MAHAJJATA SAUƘI

Hajji 2025: GWAMNA RAƊƊA ZAI JAGORANCI TATTAUNAWA DA SAURAN GWAMNONI DON SAMARWA MAHAJJATA SAUƘI

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
      Gwamna Malam Umar Dikko Raɗɗa
 Gwamnan jihar Katsina, Malan Dikko Umaru Radda ya yi kira da a yi gyara domin inganta ayyukan hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON. Gwamnan Raɗɗa ya yi kiran ne a lokacin da Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya kai masa ziyarar ban girma a masaukin Gwamnan da ke Abuja.
  Gwamna Raɗɗa ya yi tsokaci akan ayyukan Hajjin shekarar 2024 na Katsina inda ya bayyana ƙalubalen da aka samu da suka hada da illar faduwar darajar farashin kudi ga maniyyata. “A shekarar da ta gabata, ayyukan Hajji sun fuskanci matsaloli masu yawa, lamarin da ya jawo damuwa ga maniyyata da dama da kuma gwamnati baki daya. Duk da wannan kalubalen, mun yi nasarar tura alhazai kimanin 2,700 daga jihar Katsina domin sabke farali,” in ji shi.
 Gwamnan ya ba da shawarar rage lokacin aikin hajji daga kwanaki 40 zuwa makonni uku ko hudu don rage farashin kudaden da ake kashewa. “ Wani lokaci ni kan yi tambayar dalilin da ya sa ake bukatar maniyyatan mu su shafe kwanaki 40 a Saudiyya bayan aikin Hajji, yayin da wadanda ke shirye-shiryen aikin Hajjin da ake kira 'yan jirgin yawo ke kammala aikin hajji cikin kwanaki 5 zuwa 7 kacal". 
Gwamna Raɗɗa a lokacin da ya waiwaye akan batun matsalolin kiwon lafiya, yace sai da gwamnatinsa ta ƙara wa ita NAHCON kayayyakin jinya a shekarar ta 2024 da ta gabata. Sai kuma ya jaddada bukatar yin rigakafi ga maniyatan tun kafin su tafi zuwa ƙasa mai tsarki yana mai cewa, "Ina bayar da shawarar sosai da a baiwa alhazai maganin zazzabin cizon sauro kafin tashinsu domin kare kai daga matsalolin lafiya."
 Gwamnan ya kuma bayyana cewa jihar Katsina ta bayar da tallafin kudi ga maniyyatan ta a shekarar 2024 sama da Naira miliyan 500 na Hadya ta dabbobi da kuma ƙara kuɗin guzurin mahajjatan daga Dala 400 zuwa da 450 domin ganin mahajjatan sun ɗan samu sauƙin wasu abubuwan a yayin da suke gudanar da ibada. 
 Akan mu'amulla ta harkokin kudi kuwa, Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin kare alhazai da suka fito daga ƙauyuka daga hannun mazambata ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta ci gaba da bayar da tallafi a wajen musayar kudaden waje musamman Dalar Amurka da ake amfani da ita a lokacin aikin Hajji. “Zan gana da sauran gwamnonin Arewa maso Yamma domin tattaunawa kan wannan batu tare da hada kai da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin samun maslaha mai dorewa akan batun musayar kuɗaɗen waje,”inji Gwamnan na jahar Katsina ga tawagar hukumar aiyukan Hajjin ta ƙasa NAHCON a yayin wannan ziyara. 

Kamar yadda wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren yaɗa labarai na Gwamnan Ibrahim Kaula Mohammed ta ce, Gwamna Radda ya bayyana cewa, shigar da gwamnatin tarayya ta yi wajen bayar da tallafin canjin kudaden musaya a lokacin aikin Hajji na da amfani, inda ya bukaci shugaba Tinubu ya ci gaba da bayar da irin wannan tallafi. 
 A hannu guda, Gwamnan Raɗɗa ya lura da rawar da malaman addini da kafafen yada labarai ke takawa a fannin ilimin aikin hajji, inda ya bayyana kwarin gwuiwa kan ingantattun ayyuka na lokutan aikin Hajji a nan gaba.
Tun da farko, Shugaban Hukumar NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi cikakken bayani kan kokarin Hukumar na rage kudin aikin Hajjin 2025. “Ta hanyar tattaunawa da hulda da masu ba da hidima a kasar Saudiyya, mun sami damar yin tanadin kusan Naira biliyan 50 ga mahajjatan mu, kuma muna ci gaba da kokarin ganin an samu karin ragi". 
 A hasashen farko na shugaban hukumar ta NAHCON sun sanya kudin aikin Hajjin 2025 sama da Naira miliyan 10 a matsayin kudin kujera. “Saboda kokarin da muka yi mun samu nasarar rage shi zuwa Naira miliyan 8, kuma muna ci gaba da tattaunawa a kan rage kudin, in sha Allahu idan muka samu karin kudin za a kara ragewa kudin". 
 Farfesa Usman ya bayyana manyan kalubalen da Hukumar ke fuskanta, musamman kashi 2% na Babban Bankin Najeriya kan kudaden da ake turawa. “A shekarar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin naira biliyan 90, amma an cire naira biliyan 1.7 a matsayin tuhume-tuhume, la’akari da cewa adadin kudin da za a aika a bana zai kai kusan biliyan 500, za a iya cire sama da biliyan 20,” inji Farfesan
 Shugaban ya kuma kara da cewa kudaden da suka shafi sufurin jiragen sama sun kai kusan kashi 65% na adadin kudin aikin Hajji. Ya yi nuni da cewa, tuni Hukumar ta fara nuna bukatar yafewa ko rage wadannan kudade, wanda hakan na iya haifar da kara samun raguwar kudin aikin Hajji.
 Farfesa Usman a ƙarshe ya nemi goyon bayan Gwamna Radda wajen hada kan hukumomin da abin ya shafa don ganin an samu saukin wannan hajjin, yana mai jaddada muhimmancin sanya wa Musulman Najeriya saukin gudanar da aikin hajji.
 Da yake ƙarin haske, Kwamishinan aiyuka da tsare-tsare gami da Lasisi na hukumar ta NAHCON, Yarima Anofi Elegushi, ya yi cikakken bayani kan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2025. Ya kuma jaddada cewa, yayin da aka samu gagarumin ci gaba wajen rage kashe kudade a harkokin sufurin jiragen ruwa a Saudiyya, har yanzu ana fuskantar kalubalen a cikin gida.
 “Babban abin da ya fi daukar hankali a yanzu shi ne yadda za a ba da izini daga hukumomin da abin ya shafa, musamman a fannin sufurin jiragen sama, idan wadannan hukumomin suka yi mana sassauci, hakan zai yi tasiri kai tsaye kan safarar jiragen sama kuma zai rage tsadar farashin kudin Hajjin maniyyata gaba daya". 
 Kwamishinan ya sanar da cewa, biyo bayan tsauraran matakan tantance kamfanonin jiragen sama guda hudu da zasu jigilar maniyatan aikin Hajjin shekarar 2025. Jiragen sun haɗa da Flynas wanda yake mallakin ƙasar ta Saudiyya da jiragen Max Air da Air Peace da OMSA. “Kamfanonin jiragen sama 11 ne da farko suka nemi izinin shiga jigilar, amma bayan da aka yi musu tsatstsauran tantancewa, an ga wadannan hudun za su iya gudanar da ayyuka masu inganci,” in Kwamishina Elegushi

 Da ya juya akan kalubalen biyan kudaden ajiya, kwamishinan Elegushi ya bukaci gwamnatocin jihohi su yi la’akari da zuba wadannan kudade a madadin mahajjatan su. “Muna kira ga gwamnatocin Jihohin kasar nan da su fara aiwatar da zuba kudaden ajiya na maniyyatan su, wanda daga baya za a iya cirewa a yayin gudanar da sulhu, hakan zai tabbatar da cewa mun cika wa’adin da aka dibar mana ba tare da matsa wa mahajjatan da su ka biya ba,” inji shi.
 A karshe kwamishinan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a game da laifukan da suka shafi tu'ammali da miyagun kwayoyi, tare da nuna damuwa akan yadda ake kama alhazan Najeriya da haramtattun abubuwa a ƙasar ta Saudiyya, waɗanda galibin su ba tare da sun sani ba saboda ƙarancin faɗakarwa akan haka. 

Post a Comment

Previous Post Next Post