Hajj2025: KAMFANIN DA ZAI KULA DA MAHAJJATAN NAJERIYA A SAUDIYA NA SHIRIN KAI NAHCON ƘARA A KOTUN DUNIYA(ICC)

Hajj2025: KAMFANIN DA ZAI KULA DA MAHAJJATAN NAJERIYA A SAUDIYA NA SHIRIN KAI NAHCON ƘARA A KOTUN DUNIYA(ICC) 
Yayin da ake sa ran maniyata sama da dubu 52 ke shirin sabke farali a wannan shekara ta 2025 sai kuma ga wata sabuwar badaƙala na neman kunno kai wanda har ake barazanar gurfana a gaban kotun duniya ta ICC dake shari'ar manya laifuffuka a tsakanin wani kamfani Mashariƙ Al Dhahabiaj Al Mutawazi da hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON bisa zargin saɓa alƙawalin yarjejeniyar kwangilar kula da mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin da suka ƙulla. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025,ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa ta karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa.
A wasika da ya aike wa Shugaban Ofishin Aikin Hajjin Najeriya da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya a ranar Litinin 17 ga watan nan na Fabrairu, 2025, kamfanin ya zargi NAHCON da saba yarjejeniyar da suka kulla cewa kanfaninsu ne kadai hukumar za ta baiwa kwangilar aikin a bana, musamman a Mina da Arafah.
Kamfanin na Mashariƙ ya ba hukumar wa'adin kwana 20 ya koma kan sharudan yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai, idan ba haka ba ta maka hukumar a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).
Binciken wakilinmu ya gano a ranar 17 ga watan Janairu ne kamfanin da NAHCON suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da alhazan Najeriya a Kasa Mai Tsarki.
Amma daga bisani Kungiyar Hukumomin Jin Dadin Alhazai na jihohi suka daga karar cewa Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, kwanaki kadan kafin cikar wa’adin biyan kudi ga kamfanonin da kasashe suka ba  aikin.
Shugaba hukumar ta NAHCON Farfesa Abdullahi Usman Saleh ya musanta zargin yin gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, yana mai cewa hukumomin Saudiyya ne suka yi.
Ana zargin cewa NAHCON ta raba aikin gida biyu tsakanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi da kuma kamfanin Ikram Diyafa kafin cikar wa’adin ranar 14 ga watan Janairu da hukumomin Saudiyya suka sanya.
Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na zargin NAHCON da ba shi aikin kula da alhazai 26,287, duk kuwa da cewa hukumar ta sanar cewa ta samu tantunan alhazai 52,544 da za su gudanar da aikin Hajjin, wanda hakan ke nufin hukumar ta ba wa daya kamfanin aikin kula da ragowar alhazai 26,257 ke nan.
Kamfanin ya bukaci zama na gaggawa da mahukuntan NAHCON kan lamarin domin yanke shawara kan mataki na gaba da za a dauka.
Duk kokarin samun martanin hukumar NAHCON a game da wannan dambarwa da aka yi abin ya ci tura

Post a Comment

Previous Post Next Post