APC: MATASAN ƘARAMAR HUKUMAR KAITA SUN SHA ALWASHIN YIN ZAƁE CIKIN KWANCIYAR HANKALI - Tarkama
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ci gaba da yawon yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban karamar hukumar Kaita Injiniya Bello Lawal Yandaki a faɗin mazaɓun ƙaramar hukumar, matasan yankunan sun shaidawa ɗan takarar na jam'iyar APC tare da Gwamnan jahar Malam Umar Dikko Radda cewar zasu tabbatar anyi zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kamar yadda ya shaidawa wakilin mu ta wayar salula a lokacin da aka tuntuɓe shi, jagoran tafiyar matasan a yaƙin neman zaɓen Alhaji Nasiru Tarkama yace, a faɗin mazaɓu da garuruwan da tawagar suka ziyarta da suka haɗa da Girka, Adallawa, Ɗankaba, 'Yanhoho, Matsai da kuma Dankama, anyi bayanai masu gamsarwa da kuma tabbatar da cewa dukkan aiyukan da gwamnatin ƙaramar hukuma da kuma ta jaha suka fara ba' a iyar ba cikin ikon Allah za'a iyar da su. Sannan ana da yaƙinin cewa matasan ƙaramar hukumar masu bin doka da oda ne waɗanda aka tabbatar da cewa basu da wani tarihin tayar da tarzoma ta kowace fuska.
"Duk inda muka je sai mu taras matasan nan na zaman jiran isowar mu duk kuwa da cewa suna da aiyukan dake gaban su. Amma suna gaya mana cewar kawai domin zowar tamu tana cikin ƙa'ida da sunce mu yi zaman gida ba sai mun zo kamfe ba, sune waɗanda zasu fita su yi".
Malam Shi'itu, wani matashin manomi ne kuma ɗan siyasa a jam'iyar APC yace, "ai mu yanzu biyan bashi ne zamu yi musamman na zamantakewar manoma. Idan muka duba irin aiyukan alherin da wannan gwamnati tayi mana da kuma wani babban aikin da ake yi mana na madatsar ruwan nan wadda ta taso daga Abdallawa tayi kudu, gaskiya ba ƙaramin ci gaba ta fuskar noman rani za'a samu ba tunda ƙaramar hukumar ta manoman rani da na damina ce. Nan gaba muna da kyakkyawan zaton kafin wannan gwamnati ta gama wa'adinta an kafa mana kamfanin sarrafa tattasai da tumatir har a riƙa fitarwa a waje".
Shi kuwa Malam Shehu, cewa yayi a baya shi ɗan adawa ne tare da wasu abokan shi kusan su 30,amma tun daga ranar da suka gani ba labari batun aikin wancan Dam suka miƙa wuya, kuma yau an wanke su fes babu inda suke da sauran wata dauɗar wata jam'iyar siyasa. Ana dai ci gaba da yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban karamar hukumar na Kaita acikin kwanciyar hankali tare da tsaro.