YADDA AKE KOYAR DA 'YAN FURSUNA DABARUN NOMAN RANI A GIDAN GYARAN HALI A KATSINA

YADDA AKE KOYAR DA 'YAN FURSUNA DABARUN NOMAN RANI A GIDAN GYARAN HALI A KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar gidajen gyaran hali na Jahar Katsina ta ɓullo da dabarun koyar da fursunonin da take kula da su dabarun yin noman rani. Hukumar ƙarƙashin jagorancin Kwanturola Umar Baba tace, ta ɓullo da shirin koyar da noman ne domin baiwa waɗanda suka fita daga gidan bayan ƙarewar wa'adin zaman musamman matasa domin yadda zasu bayar da tasu gudunmuwar domin haɓaka noma a jahar musamman noman ranin.
Kazalika, ba noman ranin kawai hukumar take koyar da mazauna gidan ba, hatta da sana'o'in hannu irin su gyaran wayar salula, ɗunkin keke da kuma ɗunkin hular ƙube don dai tabbatar da cewa in sun fito ba zasu sake aikata wani laifin da zai sake mayar da su a gidan ba.
Shi dai wannan noman rani hukumar ta fara aiwatar daga gidan gyaran halin na shiyyar Daura. Babban abin da ake koya fursunonin a halin yanzu shi ne, noman albasa da tumatari da tattasai kasancewar jahar ta Katsina tayi suna a wannan fannin bama kamar shiyyar ta Daura, kamar yadda Kakakin hukumar ASC Najib Idris Kunduru ya shaidawa wakilinmu a Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post