Wasanni2025: LOKACI YAYI DA MATASA ZASU SAKE HIMMA A ƁANGAREN WASANNI - A.A Wali

Wasanni2025: LOKACI YAYI DA MATASA ZASU SAKE HIMMA A ƁANGAREN WASANNI - A.A Wali 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
            Alhaji Aminu Ahmad Wali 
Mataimakin shugaban ƙungiyar wasanni na matasa mai kula da shiyyar arewa maso yamma, kazalika, shugaban ƙungiyar na jahar Katsina Alhaji Aminu Ahmad Wali yayi kira ga matasan jahar akan cewa, su ƙara bayar da himma wajen ci gaba da harkokin wasanni musamman duba da irin yadda shekarar da ta wuce ta 2024. "Kowa yasan irin ƙalubalen da aka fuskanta a shekarar 2024 da ta wuce, musamman akan abin da ya shafi tattalin arziƙi da tsaro da sauran su. Amma duk da haka, matasan na jahar Katsina za'a ce sun yi ƙoƙari matuƙa ta hanyar amsa kira a duk lokacin da aka neme su"
Alhaji Wali ya ci gaba da cewa, baya ga matsin tattalin arziƙi, har ila yau, akwai bukatar daukar nauyin wasu wasannin da za'a ce kamfanoni ko masu hali sun dauki nauyi kamar yadda ake yi a wasu wuraren. "Misali, mu ɗauki ƙwallon ƙafa a irin yadda ta zama a yau. Ba gwamnati ce ke ɗaukar nauyin 'yan wasa ba. Inma har akwai abin da gwamnati ke ɗaukar nauyi bai wuce na bayar da jami'an tsaro ba a su manyan ƙasashen da muke gani. To amma mu anan har jahar Katsina har mun samu gwamnati ta shigo acikin harkar. Amma yana da kyau wasu su shigo kamar yadda nace. Shigowar ta su zai ƙara bayar da dama su kansu su riƙa tallata hajojin su. Muna da wasanni iri iri da matasan nan ke taka rawa kuma suke neman tallafi domin ƙara gogewa a harkar. Mu dubi irin yadda a yanzu suke tasowa".
Shugaban ya sake jaddada cewa, a matsayin na shugaban wannan ƙungiya zai ci gaba da bayar da gudunmuwar shi kamar yadda ya saba. Sannan ƙungiyar bayan tayi nazarin shekarar da ta wuce 2024, a yanzu suna nan suna ci gaba da shirye-shiryen wannan sabuwar shekara ta 2025 wanda suke fatan ɓullo da sabbin hanyoyi da dabaru bayan yiwa wasu garanbawul

Post a Comment

Previous Post Next Post