EFCC TA CIKA HANNU DA WASU JAMI'AN HUKUMAR TARA HARAJI A KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Jami’an hukumar shiyyar Kano na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun cafke wasu jami’an hukumar tara harajin cikin gida ta jihar Katsina su biyar bisa zargin karkatar da wasu makudan kudade N1,294,337,676.53.
Kudaden dai na gwamnatin jihar Katsina ne, an yi zargin cewa jami’an sun karkatar da su. Wadanda ake zargin dai sun hada da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu, da Nura Lawal Kofar Sauri, an kama su ne bayan da gwamnatin jihar Katsina ta shigar da kara.
Takardar koken ta zargi jami’an da hada baki wajen karkatar da kudaden shigar da ake samu daga kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da hukumar lafiya ta duniya WHO, da kungiyar likitoci ta kasa da kasa (ALIMA)
A binciken farko da hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa Rabiu Abdullahi, tsohon Daraktan tara kudi da Sakatare na dindindin na Hukumar na yanzu, ya ba da izinin bude asusun banki a bankin Sterling da sunan "BOIRS." Sunusi Mohammed Yaro daraktan asusun tattara kudaden shiga, da Ibrahim M. Kofar Soro, an nada su a matsayin wadanda su kadai suka sanya hannu a asusun.
Hukumar ta EFCC ta kuma bayyana cewa asusun ya zama hanyar farko ta karkatar da kudade zuwa ga NADIKKO General Suppliers, wani kamfani mallakin Nura Lawal Kofar Sauri, mataimakin darakta mai kula da dabarun sana’o’i da walwalar ma’aikata a hukumar. Rahotanni sun ce kamfanin ya kasance bututun da aka amfani aka sace tare da wawure kudaden. Masu bincike sun gano kudaden da aka karkatar zuwa wasu asusun banki na wadanda ake zargin.
A halin yanzu dai wadanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar EFCC na shiyyar Kano kuma ana sa ran za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta jaddada kudirinta na yaki da cin hanci da rashawa da kuma kwato kudaden jama’a, inda ta bukaci ‘yan kasar da su kai rahoton duk wani wanda ake zargi da laifin karkatar da kudade.