Da ɗumi ɗumi AMINU WALI YA ZAMA SHUGABAN IPMAN NA JAHAR KATSINA

Da ɗumi ɗumi AMINU YA ZAMA SHUGABAN IPMAN NA JAHAR KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
      A. A Wali Sabon shugaban ƙungiyar                   IPMAN na jahar Katsina 
A ranar Laraba 15/1/2025 ƙungiyar dillalan man fetur IPMAN reshen Jahar Katsina ta gudanar da zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar inda aka zaɓi Alhaji Aminu Ahmed Wali a matsayin sabon shugaba. 
Matashin ɗan kasuwar, bayan kammala zaɓen na shi, ya shaidawa 'ya'yan ƙungiyar cewa da yardar Allah basu yi zaɓen tumun dare ba. Zai tafiyar da shugabancin ƙungiyar bisa adalci tare da tabbatar da cewa, an samowa 'yan ƙungiyar duk wani haƙƙin da yake na su ne. Kazalika, yayi kira ga su shugabannin da suka gada akan cewa, su ƙara haɗa hannu domin ganin cewa an gudu tare an kuma tsira tare.
Alhaji Wali shi ne mai gidajen man A A Rahamawa. Matashin mai rajin ganin cewa matasa sun dogara da kansu har ma suna taimakawa wasu. Har'ila yau, tunasar da masu ruwa da tsaki ta wannan fuskar akan cewa, kada su manta Jahar Katsina na daga cikin manyan jihohin da ake alfahari da su wajen harkar man fetur da dangogin shi, saboda haka, a duk lokacin da wani abu ya taso, to a tuna da ita.
Wani daga cikin membobin ƙungiyar da ya nemi a sakaya sunan shi yayi kira ga sabbin shugabannin da su ji tsoron Allah a wajen harkokin tafiyar da ƙungiyar. Sannan ya jinjinawa su tsaffin shugabannin da suka sabka akan irin yadda suka tafiyar da ƙungiyar, inda yayi fatan sabbin zasu ɓullo da sabbin hanyoyin tafiyar da ƙungiyar a zamance. 

Post a Comment

Previous Post Next Post