AN ƘARAWA KAKAKIN RUNDUNAR 'YANSANDAN JAHAR KATSINA DA WASU 180 GIRMA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar Litinin 6 ga watan Janairu, 2025 rundunar 'yansandan jahar Katsina bisa jagorancin Kwamishina Aliyu Abubakar Musa, psc+ tayi bikin ƙarawa wasu jami'an ta su 181 cikin su har da Kakakin rundunar Abubakar Aliyu Sadiq girma wanda ya tashi daga matsayin ASP zuwa DSP. Kafin shi an fara da mutane biyu masu mukamin CSP zuwa ACP.
Kazalika, masu mukamin SP su 13 sun daga zuwa CSP, sai kuma wasu mutane 9 dake da mukamin DSP zuwa SP. Har'ila yau, akwai masu mukamin ASP zuwa DSP su 157.
A lokacin da yake jawabi bayan kammala azawa alamar girman ga waɗanda suka samu ƙarin girman, Kwamishina Aliyu Abubakar Musa ya ja hankalin su da cewa, su sani wani ƙarin nauyi ne na aiki ya ƙara hawa kansu wanda hakan na iya ƙara janyo ɗaukar mai wannan muƙami a tura shi wani wurin domin gudanar da aiki, wanda ciki har ana iya kai jami'in hatta da wuraren da ake fama da matsalar tsaro domin jagorantar saura don ganin anyi abin da ya kamata.
Kwamishinan har ila yau, yayi kira musamman ga matayen waɗanda suka samu ƙarin girman da cewa, kada su riƙa aza masu wasu nauye nauye ganin cewa zasu samu ƙarin albashi sanadiyar ci gaban da suka samu. CP Aliyu Abubakar ya ce, "ina kira gare ku da cewa, ku riƙa barin mazajen ku suna riƙe marayu ko 'ya'yan dangin su, kada ku ce, ba'a gama da gida ba balle a yiwa na waje. Su ma ai na gidan ne kuma baku san yadda Allah zaiyi da su ba anan gaba", inji Kwamishina Aliyu Abubakar Musa.