TAYA MURNAR YIN NASARA A KOTUN DAUKAKA ƘARA - Jamilu
Ita gaskiya sunan ta gaskiya a duk inda aka je kuma aka juya. Kazalika, hakuri shine magani kuma matakin nasara ga kowane irin al'amari. Kazalika, idan Allah ya tashi yin abu, kawai cewa yake yi, "Zamo" abin sai ya kasance a yadda ya so da kuma inda ya so.
Wannan nasara da Farfesa Tajuddeen Ebekunle Baruwa ya samu a kotun daukaka ƙarar ma'aikata akan batun cin zaben da aka yi mashi inda wasu suka nuna kin amincewar su. To Allah mai kowa mai komi ya tabbatar da wannan jagorancin kungiyar ta direbobi ta kasa NURTW ga shi Farfesa Tajuddeen.
Akan haka ni Jamilu Shu'aibu tsohon shugaban kungiyar na kananan motoci masu tafiyar dogon zango dake babbar tashar mota a Katsina nike taya Farfesa murnar samun wannan nasara tare da yi mashi addu'ar Allah yayi mashi jagora. Allah ya bashi ikon yin adalci tare da kamanta gaskiya da rikon amana. Har'ila yau, ina yin kira ga sauran membobin wannan kungiya a duk inda suke da mu taru mu bashi goyon baya tare da abokan aikin shi. Mu zamo tsinya guda. Allah ya taimaki wannan ƙungiya da shugabanninta a duk inda suke