HUKUMAR GIDAN GYARAN HALI TA JAHAR KATSINA TA SAMU SABON SHUGABA KARO NA 24

HUKUMAR GIDAN GYARAN HALI TA JAHAR KATSINA TA SAMU SABON SHUGABA KARO NA 24

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 A ranar Talata, 17 ga Disamba, 2024, CC Umar Baba ya karbi ragamar mulki a matsayin Konturola na 24 na gidan gyaran hali wanda aka fi kira da Gidan Yari na jihar Katsina. Wannan ci gaban ya biyo bayan karin girma da aka yi wa Ahmed Abdu Usman zuwa mukamin mataimakin Konturola Janar na hukumar gidajen gyaran halin(ACG) inda aka tura shi zuwa shiyyar L a matsayin Kodineta na shiyya.
 Bikin mika ragamar jagorancin wanda aka yi a takaitacce amma ya kayatarwa, ya gudana ne a hedikwatar hukumar da ke Katsina, tare da halartar jami’an rundunar. A nasa jawabin, ACG Ahmed ya bayyana godiyarsa ga jami’an bisa kwazo da hadin kai da suka ba shi a lokacin da yake aiki. Ya kuma yi kira gare su da su yi aiki tare da Konturola mai shigowa domin cimma nasarar aikin rundunar. 
 Har zuwa lokacin da aka nada shi, CC Umar Baba ya rike mukamin shugaban makarantar "Borstal Training Institute" Kano. A jawabin wa, sabon jagoran ya mika godiyarsa ga Konturola mai barin gado tare da taya shi murna bisa sabon nadin da aka yi masa a matsayin Mataimakin Kwanturola Janar na hukumar gyaran halin na kasa. CC Umar Baba ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatin sa zata dukufa wajen bada gudumawa wajen samar da tsaro a jihar ta hanyar tabbatar da cewa fursunonin da ke karkashin sa sun samu tsaro, kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin jami'in hulda da jama'a na rundunar ASC Najib Idris Kunduru ya sanarwa manema labarai ciki har da wakilin mu a jahar ta Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post