GIDAUNIYAR HILLSIDE TA KARRAMA MATASHIN ƊAN KASUWA DOKTA MUHAMMAD USMAN SARKI SABODA TAIMAKON AL'UMMA

GIDAUNIYAR HILLSIDE TA KARRAMA MATASHIN ƊAN KASUWA DOKTA MUHAMMAD USMAN SARKI SABODA TAIMAKON AL'UMMA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar Lahadi 29 ga watan Disambar 2024 gidauniyar bayar da tallafin jinƙai ta Hillside tayi bikin cika shekara da kafuwar ta, a inda ta zaɓo wasu fitattatun mutanen dake bayar da tallafi tare da gudanar da sauran wasu aiyukan jinƙai a tsakanin al'umma domin karrama masu da kambar yabo.
Kamar yadda Gwamna Malam Umar Dikko Radda wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya Alhaji Musa Adamu Dankafin Katsina ya ce, gidauniyar na aiki ne ta bin tsari da shirin gwamnatin jahar a wajen aiyukan ci gaban al'umma tare da tallafawa masu rauni musamman ta fuskar rashin lafiya ta hanyar sayan magani ana basu kyauta. Gwamnan yace, gwamnatin shi sai da ta ware naira milyan 200 domin tallafawa masu gyambon fata domin yi masu aiki tare da basu magani kyauta.
Shi kuwa Sakataren kwamitin amintattu na gidauniyar Alhaji Sufyanu Badaru Jikamshi yace, an kafa gidauniyar a ranar 29/12/2023 bisa lura da halin matsin tattalin arzikin da aka shiga wanda hakan ya janyo wasu basu iya kula da lafiyar su ta hanyar rashin samun abin sayen magani. Ya kara da cewa, gidauniyar tana bayar da tallafi akan abin da ya shafi ilmi da kuma bayar da ruwan sha a tsakanin al'umma.
Daga cikin mutanen da aka karrama a wajen wannan biki har da matashin ɗan kasuwar nan Dokta Muhammadu Usman Sarki wanda yayi suna a wajen tallafawa al'umma ta fuskoki dabam-daban, musamman ta daukar matasa wajen koyar da su walau kasuwanci ko wata sana'ar da zasu yi dogaro da kansu. Ɗan kimanin shekaru 39 zuwa 40,Dokta Sarki shi ne mai kamfanin Al-Dusar masu yin ruwan kwalba da kuma gidan ajiye namun daji (Zoo) domin sanar da matasa masu tasowa irin nau'in dabbobin da ake da su wadanda suke jin labari.
    Ɗan jarida Malam Ɗanjuma M. Katsina
Kazalika, ɗan kasuwar ya samu digirin girmamawa a jami'ar Annahada dake jamhuriyar Nijer saboda gwazon da yake nuna ta fuskar kasuwanci da kuma nunawa matasa illar zaman kashe wando.
Sauran wadanda aka karrama sun hada da su Alhaji Bilya Sanda shugaban kungiyar Abokan asibiti da kuma matashin ɗan jarida mai kamfanin "Katsina City News Malam Danjuma Muhammad Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post