DA ZA A YI AMFANI DA HADISAN GWAMNA RADDA DA AN KAWO ƘARSHEN MATSALAR TSARO - Mai masara Jibiya

DA ZA A YI AMFANI DA HADISAN GWAMNA RADDA DA AN KAWO ƘARSHEN MATSALAR TSARO - Mai masara Jibiya

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Dangane da matsalar tsaron da ake ta fuskanta wadda kullum ke sake sabon salo a wasu sassan jahar Katsina, wani matashin ɗan kasuwa yayi bayani akan irin matakan da za'a dauka don kawo karshen matsalar, matakan da a cewar sa za'ayi amfani da su ya zamo harda hadisan Gwamna Malam Umar Dikko Radda.
Alhaji Sama'ila Mai masara wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar ƙaramar hukumar ta Jibiya ya ce, "hakika Gwamna Radda ya cancanci a yaba ma shi akan irin yadda a kullum yake ta kokarin ganin cewa an kawar da wannan matsala ta tsaro ba wai acikin jaha ba har ma da ƙasa baki ɗaya. Sannan ina ganin da jama'a zasu yi amfani da hadisan shi Gwamna da tuni lamarin ya zamo tarihi".
Da yake ƙarin haske akan abinda yake nufi da hadisan Gwamna Radda, Alhaji Mai masara yace, "kowane lokaci Gwamna na nuna mana cewar dole sai mun fidda tsoro a zukatan mu mun riƙa fita muna tunkarar ɓarayin nan wadanda mutun 5 ko 6 zasu tasa sama da mutun 20 ko 30 zuwa daji su yi masu duk wulakancin da suka daga karshe ma su kashe na kashewa. Gwamna yana tunasar da mu cewar mutuwar nan dai guda ce kuma kowa sai yayi ta, to don me zamu rika bari ana cin zarafin mu saboda an riƙe bindigar da bata wuce 3 a hannu ba. Muddin zamu yi ƙumumuwa zamu rufe su mu ƙwace duk wani makamin da suke da shi. Cikin mu ba'a san wanda Allah ya ba wata rahama ba, su harba bindigar ta ƙi tashi. Ayi haka sau biyu ko ukku aga in basu san nayi ba". Matashin ɗan kasuwar ya ƙara da cewa, nuna tsoron ya taimaka wajen basu karfin yiwa jama'a abinda suka ga dama. Sannan tona asirin masu ba barayin bayanai shi ma ya zama wajibi don ance da ɗan gari kan ci gari.
Alhaji Sama'ila ya kara yabawa Gwamna Radda akan irin yadda ya jajirce wajen ganin kasuwancin Jibiya ya sake farfadowa ta irin yadda ya kafa kwamiti karkashin shugabanci shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jahar Honarabil Jabiru Salisu Tsauri inda suka zauna da duk wani jami'in tsaron dake da hannu don ganin an sakar masu mara sun ci gaba da harkokin kasuwancin su. " Da mun dauka kamar an fidda mu daga Najeriya bayan su Nijer basu amshe mu ba. Buhun dussa in zaka dauko shi daga Katsina zuwa Jibiya wani tashin hankali ne. Amma yanzu sai mu ce Alhamdulillahi", inji Alhaji Sama'ila Mai masara shugaban kungiyar yan kasuwar Jibiya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post