BABU ƘANSHIN GASKIYA AKAN LABARIN DA AKA YADA DA SUNAN MUTANEN JIBIYA AKAN KASHE WANI DAN BOKO HARAM - Ƙungiyar tsaro

BABU ƘANSHIN GASKIYA AKAN LABARIN DA AKA YADA DA SUNAN MUTANEN JIBIYA AKAN KASHE WANI DAN BOKO HARAM - Ƙungiyar tsaro
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Wani labari da wasu jaridun kasar nan suka yada inda aka baiyana kashe wani jagoran kungiyar Boko Haram mai suna Abu Sale wanda aka mayar da shi dan bindigar daji wanda ya addabi yankin karamar hukumar Jibiya da cewa wannan labarin babu kanshin gaskiya acikin shi kuma cin zarafin al'ummar jama'ar karamar hukumar Jibiya ne gami da kara tura su cikin wani halin na rashin tsaro.
Labarin wanda jaridar Blueprint ta wallafa a ranar 26 ga watan Nowamba, 2024 wanda wakilinta Benjamin Samsun ya rubuta, ta baiyana cewa kungiyar masu rajin kare yankin Jibiya mai suna Muhammadu Magayaki yayi bayani a madadin al'ummar Jibiya ya jinjinawa karamin minisan tsaro na Najeriya Bello Mutawalle akan irin yadda ya jajirce wajen daukar matakin kawo karshen aiyukan ta'addanci a yankunan arewa maso yamma wanda hakan yayi sanadiyar kashe shi Abu Sale wanda yake daya daga cikin manyan 'yan ta'addan da suka addabi yankin musamman ita karamar hukumar ta Jibiya wanda yace, sunyi farin ciki da wannan mataki.
Saidai wata sanarwa da ta fito daga kungiyar dake tallafawa tsaro a karamar hukumar ta musanta wancan labarin. A cewar kungiyar wadda Sakataren kungiyar Kabir Sani ya sanyawa hannu ta ce, bakin binciken su babu wani mutum mai suna Muhammad Magayaki balle labarin kashe wancan ɗan ta'adda da aka ambata. "Bakin iya binciken mu babu wani abu da yayi kama da wannan labarin balle wanda aka ambata da sunan mutanen Jibiyar ko kisan wancan mutun da aka ambata. Har yanzu muna cikin matsalar tsaron nan wanda kusan kullum sai mun fuskanci wannan matsalar.
Kamar yadda wani bincike ya baiyana mana, shi dai wancan dan ta'adda mai suna Abu Sale wani jagoran kungiyar Boko Haram ne ba ɗan bindigar dajin da suka addabi wannan yanki ba ne. 

2 Comments

  1. Wannan maganar banace
    QARYA yakayimana mu mutanan jibia local government katsina state

    Kuma Allah yarsinema duk Wanda ya yadawannan labarin
    AMEEN YAHAYYU YAQAYYUUM

    ReplyDelete
  2. Babu wani shugaban boko haram da aka kashe bagaskiya bane domin kuwa kusan kullum sai barayi sunshigo jibia sunkashe nakashewa sun kora wasu cikin daji kuma sun raunata wasu

    ReplyDelete
Previous Post Next Post