ANYI KIRA GA MASU NIYAR AIKIN HAJJIN 2025 NA JAHAR KATSINA DA SU CI GABA DA AJIYAR KUDIN SU A BANKI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina karkashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ta yi kira ga masu son zuwa aikin Hajjin 2025 da su fara bayar da kudin ajiya na naira milyan 8 da dubu dari 4 a bankunan da aka amince da karbar ajiyar tun kafin lokaci ya kure.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama yayi wannan kira a wata ziyarar aiki da ya kai a gidajen rediyo da talbijin mallakar gwamnatin jahar ta Katsina kamar yadda wata sanarwa ta fito daga ofishin Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya sanyawa hannu. Daraktan hukumar ya shaidawa manyan manajojin gidajen yada labaran cewa ya kawo wannan ziyara ne tare da mukarrabansa domin karin neman hadin kai da goyon baya kamar yadda gidajen suka saba bayarwa hukumar. Alhaji Dankama har ila yau, ya jinjinawa gidajen akan irin yadda suka rika yada labaran aiyukan hukumar musamman akan aikin Hajjin 2024 da ya gudana wanda kuma shi ne aikin farko da shi Daraktan ya jagoranta bayan bashi wannan gagarumin aiki da Gwamna Malam Umar Dikko Radda ya yi.
"A gaskiya babu abinda zamu cewa wannan kafa domin nuna farin cikin mu illa yi maku addu'ar fatan ci gaba da samun nasara a duk lokacin da kuke gudanar da aiyukan ku. Har'ila yau, ba tare da gajiyawa ba, wannan hukuma na kara neman hadin kan ku da wayar wa da jama'a kai tare da karin yin kira musamman ga masu son zuwa aikin Hajji na 2025 da suyi hanzarin kai kudaden ajiyar su ga bankuna kamar yadda ita hukumar dake kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta bayar da umarnin yi kafin nan da wani É—an lokaci. Mai son zuwa zai fara ajiye naira milyan 8 da dubu dari 4. Wadanda kuma suke da kudaden su a hannun hukumar da basu samu damar zuwa a 2024 suna iya ci gaba da zuba sauran kudin har su kai adadin da aka baiyana",inji Alhaji Yunusa Dankama.
A nasu jawaban, manajojin gidajen rediyon da talbijin, Alhaji Lawal Attahiru Bakori da Alhaji Abba Zaiyana sun tabbatarwa da Babban Daraktan ci gaba da ba hukumar goyon baya da hadin kai. Dukkan su sun baiyana irin yadda suka gamsu da aikin Hajjin 2024 da ya gabata musamman a irin yadda suka ba wakillan su goyon baya wajen gudanar da aikin su a lokacin tashi da kuma sabkar mahajjatan jahar.
Daga cikin daraktocin da suka rufawa Babban Daraktan hukumar baya akwai Daraktan kudi Alhaji Sagir Abdullahi Inde(Sarkin Musawa), Daraktan tsare-tsare Alhaji Yusuf Ahmed sai Daraktan Mulki Alhaji Nasiru Ladan da Babban mai bincike na cikin gida Alhaji Lawal Kurabau.
Indai za'a iya tunawa, hukumar dake kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta umarci sauran hukumomin alhazan na jihohi da su fara karbar kudaden ajiya ga maniyatan na naira milyan 8 da dubu dari 4 kafin karshen watan Disambar 2024 domin bayar da damar ci gaba da shirye-shiryen aikin acikin lokaci kamar yadda ita kasar Saudiya ta bukaci kasashe su yi. Akan haka ne, shi ma Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda ya ba hukumar dama da ta fara karbar wadannan kudaden ta hanyar takardun bankin da aka kai ajiyar.