NAHCON TA WARE KUJERU 1,288 NA AIKIN HAJJIN 2025 GA JAHAR YOBE
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ware kujeru 1,288 a jihar Yobe domin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2025 zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da wakilin mu a ofishinsa da ke Damaturu kan yadda aka gudanar da aikin hajjin bana da kuna wadda za'a gudanar a shekara mai zuwa ta 2025.
Ya ce, a kwanakin baya ne hukumar ta gudanar da wani taro da mahukunta da ma’aikatanta da daga fadin kananan hukumomi Jihar 17 inda suka bayyana rabon kujerun da aka baiwa jihar na 2025.
Mai Aliyu ya bayyana cewa, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta shaida musu cewa, mai yiwuwa su samu kari idan lamarin ya tabbata, amma a halin yanzu sun ba jihar Yobe kujeru 1,288 na kujerun aikin hajjin 2025.
'Ya bayyana cewa, sun raba kujerun ne bisa tsarin da hukumar ta tsara a jihar.” Don haka ne muka gana da jami'an mu da ke karbar kudin kujerun aikin hajjii a kananan hukumomi 17 da kuma masu karbar kudi a hedikwatar hukumar da ke nan Damaturu'
“Muna da ragowar maniyyatan da suka fara biya amma ba su Kai ga kammala biya a shekarar 2024 su kimanin 180, yanzu za mu mika sunayen su kai tsaye, suna da kujeru saboda kudinsu na tare da mu maimakon mayar musu kudaden su in har ba sune ke bukatar hakan ba, a halin yanzu kan hakan mun ce, muna jiran hukumar NAHCON ne, domin mun riga mun aika musu da kudaden su tun a baya da zarar sun dawo mana da su za mu tuntube su.” inji Mai Aliyu.
Ya kara da cewa, kudin ajiyar kujerar aikin Hajjin 2025 a yanzu ya kai miliyan takwas da dubu dari biyar (N8,500,000) ya kara da cewa, abin da NAHCON ta bukaci su sanar ke nan .
“A matakin mu, wanda duk ya ke da sha’awar aikin hajjin 2025, ya fara biya domin duk wani kudi da za mu samu daga kowane maniyyacin Jihar Yobe, shi ne naira miliyan 8,500,000, kuma mutum yana iya zuwa don biya a matakin kasa ko Jiha da kananan hukumomin kamar yadda aka yi a bara 2024, "in ji Mai Aliyu.
Don haka ya kirayi dukannin wadanda ke da niyyar sauke farali da su yi kokarin kawo kudaden su don adana su akan lokaci don su zama cikin lisaafi.