GWAMNA RADDA YA SHA ALWASHIN TALLAFAWA 'YAN APC DA SUKA BAYAR DA GUDUNMUWAR SU A LOKACIN YAKIN NEMAN ZABEN SHI

GWAMNA RADDA YA SHA ALWASHIN TALLAFAWA 'YAN APC DA SUKA BAYAR DA GUDUNMUWAR SU A LOKACIN YAKIN NEMAN ZABEN SHI 
 Kokarin da yake na tabbatar da Kara Hadin Kai da Zumunci tsakanin Yan Jam'iyyar APC Na Kananan Hukumomin Jihar Katsina Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina ya Kara Jaddada Goyon Baya Da tallafama Yan Jam'iyyar Musamman Wadan da Suka Bada Gudunmawa Wajen Gwagwarmaya a lokacin Da ya fito takarar Gwamnan Jihar katsina.
Wannan bayanin na kunshe daga bakin Shugaban Kwamitin Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama wanda Maigirma Gwamnan Mallam Dikko Umar Radda phD ya azawa nauyin tattaunawa da wasu 'yan siyasar da suka fito daga Shiyyar Katsina. Shugaban kwamitin wanda kuma shi ne Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar katsina ya baiyana yunkurin Gwamnan a wani taron da ya gudana a dakin taro na hukumar. 
Shugaban kwamitin Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya shaidawa mahalarta taron irin manufofin Gwamna Radda da gwamnatin shi tare da yin godiya akan irin jajircewar da gudunmawar da suka bada musamman a lokacin zabe tare da tabbatar da nasarar Jam'iyyar APC a Jihar katsina.
Ya kara da cewa, idan basu manta ba yayi masu alkawali wanda kuma yanzun ne yake ta kokarin sauke wannan nauyin alkawali da yayi masu.
Mallam Dikko Umar Radda phD ta bakin shi shugaban kwamitin Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya kara kira a garesu da su zama tsintsiya madaurin ki daya tare da cigaba da ba gwamnati goyon baya da Addu'a kamar yadda ya nemi mahajjatan da suka je sabke farali a 2024 su yi domin fuskantar wannan kalubalen rayuwa da matsalolin tsaro da ake fama da ita. Alhaji Yunusa Dankama bai karasa bayanin shi ba sai da ya sake jinjinawa Gwamna Radda akan irin gudunmuwar da ya bayar a lokacin aikin Hajjin 2024 da ya gabata, musamman biyan hadaya ga maniyatan da kuma sauran abubuwan jin dadi domin ganin sunyi aikin su cikin nasara, abin da kuma ya faru kenan. 
A nashi jawabin Sakataren Jam'iyyar APC na Jihar Katsina Barister Namadi ya jinjina ma Gwamnan Jihar katsina akan ayyukan alkhairi da yake gudanarwa a fadin Jihar katsina.
Barister Namadi wanda yayi dogon bayani akan kokarin da wannan Gwamnati keyi na bunkasa rayuwar al'ummar Jihar Katsina baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post