..ZA MU KAWO KARSHEN YAWAITAR KANANAN MAKAMA DA SAFARAR HARAMTATTUN KAYA AKAN IYAKOKIN MU" - Hukumar Kwastam
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar hana fasa kwabri da aka fi sani da Kwastam ta Najeriya ta sake nanata shirinta na kawo karshen yawaitar kananan makamai da kuma safarar haramtattun kayayyaki a tsakanin al'ummomin kan iyakokin kasar.
Ko’odinetan hukumar NCS mai kula da shiyyar B, Kaduna, Sambo Dangaladima, ya nanata shirye-shiryen rundunar na yaki da wannan ta’addanci a lokacin da yake jawabi ga jami’an rundunar na jihar Katsina a ranar Larabar nan.
Ya ce hukumar ta NCS a karkashin kulawar CGC Bashir Adeniyi, ta dauki matakan da suka dace don magance kwararar kananan makamai a yankunan kan iyaka. Ya kara da cewa hukumar ta NCS ta dauki matakan da suka dace don karfafa ayyukan sa ido a kan iyakokin kasar don yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da aikata laifuka.
Dangaladima ya ce: “Mun himmatu wajen tabbatar da mutunta iyakokinmu yadda ya kamata da kuma hana shigowar haramtattun kayayyaki, da kuma yaduwar kananan makamai da ka iya shiga hannun ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka.”
Akan jindadin hafsoshi da sauran jami'an, Kodinetan na shiyyar ya ce Adeniyi yana sane da wahalhalun da jami’an su ke ciki kuma sun himmatu wajen inganta rayuwarsu. A cewarsa, ma’aikatar karkashin Adeniyi ta ci gaba da jajircewa wajen samar da dabarun jagoranci don tabbatar da isar da sahihanci mai inganci da ingantaccen aiki.
Don haka ya bukaci jami’an hukumar da su kara himma wajen ganin hukumar ta NCS ta samu gagarumar nasara a ayyukan ta na samar da kudaden shiga, da dakile fasa kwauri, da kuma saukaka harkokin kasuwanci.
Dangaladima, wanda ya ce ya zo Katsina ne domin wayar da kan jami’an kan muhimmancin hadin kai, kirkire-kirkire da kuma alakar masu ruwa da tsaki da hukumar kwastam ta Najeriya, ana sa ran zai gana da ‘yan kasuwa da na kan iyaka.
Tun da farko, Shugaban hukumar na yankin Katsina Kwanturola Abba-Aji, ya ce jihar na da yankunan kan iyaka 12 da ba su aiki sai kan iyakar Jibia da aka bude kwanan nan don gudanar da harkokin kasuwanci.