Da dumi dumi AN SASSAFTA DOKAR HANA FITA A JAHAR KATSINA

Da dumi dumi AN SASSAFTA DOKAR HANA FITA A JAHAR KATSINA

 Daga Kabir Ahmed S/Kuka
 Biyo bayan dokar hana fita daga karfe 7 na dare zuwa karfe 7 na safe a duk fadin Jahar Katsina sanadiyar zanga-zangar matsin rayuwa da ake yi a fadin kasa baki daya wadda aka samu barna da asarar rayuka da aka yi a wasu jihohin. A yanzu gwamnatin Jahar Katsina ta sassafta lokacin da wannan doka zata fara aiki, maimakon karfe 7 na dare ta koma karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safe. Mukaddashin Gwamnan Jahar Alhaji Faruk Jobe ne ya amince da wannan sassafci bayan zama da yayi da jami'an tsaro inda aka samu rahoton samun sauki da kuma raguwar matsalar tsaro, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Barista Abdullahi Faskari wadda Daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Abdullahi Aliyu 'Yar'aduwa ya sanyawa hannu.

Post a Comment

Previous Post Next Post