MATA SAMA DA 200 MAHAJJATAN JAHAR KATSINA SUN YI DAWAFIN ADDU'O'I NA MUSAMMAN GA JAHA DA KASA

MATA SAMA DA 200 MAHAJJATAN JAHAR KATSINA SUN YI DAWAFIN ADDU'O'I NA MUSAMMAN GA JAHA DA KASA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Rahotannin da suka shigo mana daga garin Makka na cewa mata mahajjata sama da 200 suka je Harami a yammacin Juma'ar inda suka yi Dawafi na musamman domin yiwa jahar ta Katsina addu'o'in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da samun ci gaban arziki.
Matan wadanda suka samu jagorancin wasu matan ma'aikatan hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina, wato, Malama Binta mai Larabci da Malama Hauwa, matan sun ce wannan kuduri nasu na daga cikin alkawalin da suka daukarwa Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda na yiwa jahar addu'o'in wadanda suka hada har da shi kanshi Gwamnan, Shugabannin da suka jagoranci aikin Hajjin da sauran shugabannin jahar ta Katsina baki dayan su.
Matan wadanda suka baiyana cewar inda akwai abin da ya fi yin Dawafin don yin wadannan addu'o'i to da sun je sun yi domin nuna godiyar su akan irin kulawar da suka samu a lokacin da zasu aiwatar da wannan aikin, kulawar da suka fara samu tun daga can gida Katsina. ASKGLOC NEWS mun yi kokarin jin ta bakin wasu matan ta wayar salula bayan jin wannan labari don jin ta bakin su. Hajiya Halima ta ce, "mun yanke wannan shawarar zuwa yin wannan Dawafi a wannan rana ta Juma'a domin muhimmancin ta. Kazalika, mun roki Allah da ya kawo mana karshen iftila'in dake muke ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa. Sannan duba da irin yadda shi Gwamna yayi mana hidima akan wannan aiki, musamman dauke mana nauyin yin hadaya ga kuma goron salla na Riyal 400 wanda ba karamin taimaka mana yayi ba, bama kamar gare mu mata wanda ba sai na fadi ba, kasan muna son yiwa iyali tsaraba to kuma sai ga tsadar da ake fuskanta hatta anan kasar".
Ita ma wata mahajjaciyar wadda ta ce ta fito daga karamar hukumar Kaita ce, duk da ta ce ba sai ta ambata sunan ta ba, ta shiga cikin sahun sauran 'yan-uwanta a lokacin da ta ji suna wannan shiri domin yin wannan Dawafi na musamman. "Lura da irin halin da jahar mu take dangane da batun tsaro da kuma irin yadda Gwamnan ya mayar da hankali na ganin ya ceci rayukan al'umma bakin iyawar shi, to, duk wani mai tunani, musamman mu mata da ake bari da marayu inma har mun tsira daga tozarcin wadannan 'yan ta'adda, dole mu fito mu yi addu’ar. To kuma sai gashi Allah ya kawo inda ake karbar addu'ar babu wani shamaki. Gaskiya muna godiya ga Gwamna da kuma É—an majalisar mu na Kaita wanda shi ma ya kawo mana ziyara ya kuma bamu tallafi".
Indai za'a iya tunawa, Gwamna Radda ya bukaci mahajjatan da su yiwa jaha da kasa addu'o'in zaman lafiya da ci gaba. Har'ila yau, ya roke su da su yi mashi addu'ar Allah ya ci gaba da bashi karfin imani domin yayi mulkin shi bisa adalci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post