Hajj2024: ZA A FARA AWON MANYAN JIKKUNAN ALHAZAN JAHAR KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Yayin da ake ci gaba da kwaso mahajjatan Najeriya zuwa gida bayan kammala aikin Hajji na 2024, yanzu haka rahoton da ya shigowa ASKGLOC NEWS hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina karkashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ta yi nisa a bisa shirye-shiryen fara awon manyan jikkunan mahajjatan domin fara shirin dauko su zuwa gida.
Kamar dai yadda aka saba, awon manyan jikkunan alhazan yana nuna alami ne na fara kwaso su zuwa gida daga kasa Mai tsarki bayan kammala aikin hajji. Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya tabbatarwa da wakilin mu a lokacin da ya tuntube shi cewar, lallai hukumar na ci gaba da tsaren-tsaren fara awon manyan jikkunan da kuma sauran shirye-shiryen yadda za'a fara kwaso mahajjatan zuwa gida.
Saidai kamar yadda aka sani ga shi wannan aiki na ibada, kafin maniyaci ya tafi yana nuna zakuwar shi na ganin ya tafi, haka zalika, a lokacin da aka kammala aikin babu abin da yake so illa yaga ya dawo gida. To su ma mahajjatan na jahar basu wuce shiga irin wannan halin ba wanda ya samo asali tun daga lokacin da aka fara zuwa aikin na Hajji. Kusan duk mahajjacin da muka tuntuba don jin ta bakin shi, babu amsar da zai bayar sai batun dawowar shi gida. Kazalika, wani abin da muka lura da shi a wannan aikin na wannan shekarar shi ne, zamowar jajar ta Katsina ita ce jaha ta karshe da aka dauki maniyatan naka domin zuwa wannan aikin, wanda kuma ita ce jahar ta karshe a Najeriya da za'a kwaso mahajjatan ta zuwa gida a bisa tsarin da ita hukumar kula da aikin Hajji NAHCON ta shirya.
Saboda ba'a taba samun cewa jahar koda na biyun karshe ne ta zo a wajen gudanar da aikin yasa wasu ke ganin abin baiyi masu dadi ba, bayan kuma wani abu ne dake juyawa kamar yadda aka taba fara aikin shekarar a wannan jaha.
Har ika yau, wani labarin da muka samu na cewa, domin kara karfafa mahajjatan kwarin guiwar ci gaba da yin ibada, malaman dake tare su sun ci gaba da yiwa mahajjatan wa'azi da fadakarwa na su ci gaba da zuwa suna yin Dawafi tare da addu'o'i domin wata dama ce da ba kowa ke samun ta ba. Mahajjatan dai basu gushe ba wajen yiwa jahar tare da shi Gwamna Radda addu'a ba ta samun nasarar kawo karshen aiyukan ta'addanci a duk fadin jahar wadda Gwamnan yake aiwatarwa a yanzu. Kazalika, sun jinjinawa jami'an da suka jagorance a wajen aiwatar da wannan aiki ta yadda suka zauna tare da su da kuma sauraren su akan duk wani batun da suka kawo masu domin daukar mataki.