Hajj2024 A WAJEN MU GWAMNA RADDA NE GWAMNAN ALHAZAN JIHOHIN AREWA TA YAMMA - Nasiru Tarkama
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Wani mahajjaci daga jahar Katsina mai suna Alhaji Nasiru Tarkama ya shaidawa wakilin mu ta wayar salula a tattaunawar da suka yi shi cewa, Gwamnan jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda shi suka kalla a matsayin Gwamnan alhazan jihohin arewa maso yamma na Najeriya. "Dalilan da suka sa nace haka sun hada da irin bayanan da muka ji daga wasu mahajjatan da suka fito daga mafi yawan akasarin wadannan jihohi. Farko dai shine, gwamnan da ya fara daukewa mahajjatan shi mu 2760 yin hadaya. Sannan shi ne Gwamnan da hatta abincin da ake bamu a Makka shine ya dauki nauyi sannan kuma yasa aka warewa masu wata lalura irin nasu abincin. Idan muka dauki zaman mu a Minna, irin yadda muka ga wasu mahajjatan na shan wuya musamman ta wajen abinci da abin sha da makwanci, mu a jahar Katsina bamu fuskanci wannan matsala ba sai dan abinda ba'a rasa ba".
Alhaji Nasiru ya kara da cewa, saboda wadatar abinci da abin shan da suke da shi a wannan zama na Minna har abokan arzikin da suka hadu da su na wasu jihohin suka rika taimakawa. Sannan yace, irin yadda jahar ta Katsina tayi tsarin wannan aiki a can Saudiya sai ga shi har wasu suka fara kwaikwayo.
"Kowa yasan irin yadda aikin wannan shekara ya zo da tsada, to, ina tabbatar maka da anan kake yanzu maganar nan da muke yi da kai da ka sha mamakin ganin irin yadda mahajjatan jahar Katsina ke cikin walwala da nishadi. Kuma bakin gwargwado muna ta sayen kayan tsaraba saboda irin tallafin da muka samu na Riyal 400 kowane mahajjaci. Wannan ma yasa wasu mahajjatan sun taya mu da yi mashi addu'a akan irin yadda Gwamnan yake yiwa al'ummar shi.
Da ya juya akan yadda hukumar jin dadin Alhazai ta jahar ta shirya yadda aka gudanar da wannan aikin,Alhaji Nasiru yace, "to duk da wannan shi ne zuwa na na farko, amma gaskiya jami'an wannan hukuma karkashin jagorancin shi Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama sun yi abin a yaba masu kwarai da gaske. Tabbas a lokaci zuwa lokaci sukan kai ziyara a dukkan gidajen da muke domin jin ko muna da wani koke ko wata matsala. Shi kan shi Amirul Hajjin Maigirma tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Tukur Jikamshi baiyi kasa a guiwa ba tare da mukarraban da shi kan shi shugaban hukumar jin dadin alhazan Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai, gaskiya suna zuwa wurin mu domin yi mana wani bayani ko ji daga bakin mu in akwai wani abu. Su kansu Malaman da aka turo gaskiya wasu lokuttan da makwabtan na wasu jihohin muke zama sauraren wa'azin su idan suna yi mana. Wani abinda ya kara burge ni shi ne, bangaren mata ma'aikatan wannan hukuma, musamman wajen yiwa mata 'yan uwansu taron bita, abin gaskiya mun ji dadin shi sosai. Sannan wannan haduwa da muke yi tare da wasu makwabtan namu in ana wani abu na karuwa, nan naji suke cewa, su gaskiya da dan wata jaha na da damar ya zabi wata jahar da zai tashi a lokacin aikin hajji, to su basu da wani wuri da ya fi jahar Katsina. Wannan ziyara da Gwamna ya kai mana a zaman mu na Minna gaskiya ba karamin tasiri abin yayi ba, domin wasu na cewa, shi kadai ne Gwamnan da ya fara kaiwa alhazan shi ziyara irin wannan", inji Alhaji Nasiru Tarkama.