HAJJI 2024: WAKILLAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA SUN ISA MAKKA DON TSARA MASABKAN MANIYATAN JAHAR

HAJJI 2024: WAKILLAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA SUN ISA MAKKA DON TSARA MASABKAN MANIYATAN JAHAR
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Yadda É—akunan maniyatan jahar Katsina suke a garin Makka
 Yayin da jigilar maniyyata aikin hajjin bana na jihar Katsina ke kara kusantowa, tawagar wakillan hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina ta isa birnin Makkah. 
Tawagar wacce ta ƙunshi membobin hukumar da ma'aikatan hukumar karkashin jagorancin shugabancin kwamitin hukumar Alhaji Abdullahi Darma da mataimakin shugaba Alhaji Aliyu Umar Radda, yayin da Hassan Ibrahim Bindawa yake a matsayin sakataren kwamitin. Sauran sun hada da Isa Yandaki, Yusuf Isma'Il kaita da Hajiya Nafisa Doguru.
 Bayan isar tawagar birnin Makkah ne suka gudanar da aikin Umrah kafin su fara yiwa masabkan da za'a baiyawa alhazan jahar lambobi tare da rabon dakunan bisa ga ka'idojin NAHCON da kuma hukumomin kasar ta Saudiyya, kamar yadda Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya sanar.
Ana dai sa ran fara jigilar maniyatan na jahar Katsina su dubu 2760 zuwa kasar ta Saudiyya nan bada jimawa ba don sabke farali. 

Post a Comment

Previous Post Next Post