Hajj2024 HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA TA CANCANCI YABO - FAAN

Hajj2024 HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA TA CANCANCI YABO - FAAN
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

An jinjinawa hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina karkashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama da kuma sauran jagororin da suka jagoranci shirye-shirye da tsare-tsaren da hukumar tayi don ganin an aiwatar da aikin Hajjin na bana cikin nasara.
Babban Manajan hukumar dake kula da sabka da tashin jiragen sama FAAN ta kasa dake kula da filin jirgi na Umaru Musa 'Yar' aduwa anan Katsina Alhaji Usman Lawal Usman ne yayi wannan yabo a hirar shi da wwkilin ASKGLOC NEWS.
"Gaskiyar magana, mu anan FAAN ba zamu ce komi ba dangane da yadda aka gudanar da daukar maniyatan jahar Katsina a wannan shekara ta 2024 in muka kwatanta da shekarar 2023 saidai godiya. Irin tsarin da aka taho da shi musamman ta yadda shi Amirul Hajj Maigirma tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Tukur Jikamshi ya jajirce na ganin an gudanar da aikin kamar yadda aka tsara. Tabbas Amirul Hajji yayi aiki kafada da kafada da sauran jami'an hukumar da suka hada da shi Shugaban hukumar Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai da shi Babban Daraktan Alhaji Yunusa Dankama da sauran masu ruwa da tsaki na aikin wadanda a mafi yawan lokutta zasu zo a lokacin da ake daukar alhazan. Kusan ma ince babu jirgin da zai tashi ba tare da kaga wadannan shugabannin ko wakillan su sun zo ba".
Babban Manajan wanda yace, daga cikin tsare-tsaren da suka fi burge su kuma suka sanya aikin nasu ya zo cikin saukin sun hada da kawo alhazai filin cikin lokaci domin kwasar su zuwa kasar Saudiya. "Kasan muna amsar kudi a can bakin kofa ga duk wani abin hawan da ya zo shigowa musamman a wannan lokaci na aikin Hajjin, amma irin yadda muka ga shi Amirul Hajjin ya dauki mataki akan korafin da muka yi a daya daga cikin tarurrukan da muka yi da su, wato, na cinkoson 'yan rakiya wanda sukan zo su cika filin har ma a wani lokaci sukan so fin alhazan yawa, sannan ta nan ne ake samun kawowa alhazan wasu kayan da aka haramta tafiya da su. Ga kuma bata wuraren zagayawa da aka tanadar su maniyatan. To a wannan karon sai muka hakura da wadancan 'yan kudaden shiga da muke amsa,kuma gaskiya an dauki mataki kuma abin yayi tasiri matukar gaske".
Da ya juya ga batun yadda filin jirgin yake a yanzu musamman a sashen da ake sabkar da maniyatan kafin zuwan jirgi, Alhaji Usman yace, bayan ya kai koke ga can babban ofishin su na kasa, cikin dan lokaci aka zo aka yi gyare-gyaren da suka kamata, kamar sanya na'urar sanyaya wurin zama, gyaran wuraren zagayawa,tare da kara samun damar tayar da injinan su a lokacin sabka da tashin jirgin da zai dauki maniyata. 
"Naje munyi magana da hukumar bayar da hasken wutar lantarki KEDCO dake nan Katsina inda muka yi magana da su akan cewa, koda ba lokacin bamu wutar ba ne, indai har jirgin da zai dauki maniyatan zai zo, to in kira su awa daya kafin ya sabka zasu bamu wuta har sai ya tashi, kuma haka muka yi duk da cewa a wasu lokuttan sai mun tayar da manyan injinan mu saboda rashin karfin wutar lantarkin"
Babban Manajan ya ce, lallai ya gamsu matuka ga irin yadda aka tafiyar da aikin na bana musamman ta fuskar tsaro inda ya yabawa kowane sashe na jami'an tsaron da suka yi aiki a fannonin su. "Hatta da sojojin dake nan filin sun bayar da gudunmuwar su wajen ganin anyi aikin lafiya. Shi kan shi sashen da ake sabkar da manyan baki matafiya mun samu damar yin amfani da shi domin samarwa su manyan jami'an hukumar jin dadin alhazan wajen zama a lokacin da ake jigilar kafin tashin jirgin ba kuma tare da an karbi ko kwabo kamar yadda aka san yadda wurin yake".
A karshe Alhaji Usman Lawal Usman Babban Manajan filin jirgin sama na Umaru Musa 'Yar' aduwa bayan ya jinjinawa Gwamna jahar Malam Umar Dikko Radda ta irin gudunmuwar da ya bayar a wajen ganin anyi aikin cikin nasara, kazalika, yayi fatan samun hadin kai da goyon baya tare kuma sake bin hanyoyin da aka bi aka samu nasarar kwasar maniyatan zuwa kasa mai tsarki acikin nasara da tsari, haka ma a samu a lokuttan dawowar su. Sannan yayi kira ga sauran jama’a musamman masu zowa tarbar alhazan a lokacin da zasu dawo gida. "Muna fata za'a bi doka da oda ta yadda anan ma za'a samu nasarar gama aikin kamar yadda aka yi a lokacin tafiyar su", inji Alhaji Usman Lawal Usman Babban Manajan filin jirgin sama FAAN na Umaru Musa 'Yar'aduwa dake cikin garin Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post