Hajj2024 ANYI KIRA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA DA SU CIGABA DA YIN HAKURI DA JUNA - Safara'u Masari

Hajj2024 ANYI KIRA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA DA SU CIGABA DA YIN HAKURI DA JUNA - Safara'u Masari
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
A Yayin da maniyatan jahar Katsina na jirgin farko da biyu suke Birnin Madina a halin yanzu don cigaba da gudanar da ziyarorin su, Shugabar kwamitin dake da maniyatan a Madina Hajiya Safara'u Masari wadda kuma take daya daga cikin membobin hukumar Jin dadin Alhazan ta shawarci maniyyatan da su zamo masu ci gaba da hakuri da Junan su a lokacin da suke cigaba da aiyukan ibadar su a nan Kasa mai tsarki. 
Ta fadakar da maniyyatan da su zama Jakadu na gari a duk inda suka tsinci kansu a wannan Kasa domin kare mutuncin su da jahar su da kuma kasa baki daya. Ta kara da yi masu fatan Alheri da addu'ar Kowanen su yayi aikin Hajji karbabbe.
Shi ma Alhaji Saminu Baure daya daga cikin membobin hukumar ya kara jan hankalin maniyyatan da su ci gaba da yiwa kansu,iyalan su da kuma shugabanni addu'a domin samun zaman lafiya, karuwar arziki da kuma samun nasarar aikin da suka zo yi na ibada. Kazalika, ya shawarce su da cewa su rika tafiya a dunkule a duk inda zasu je tare da katin shaidar su mai dauke da hotunan su domin kaucewa shiga cikin wata matsala ko wani yanayi na daban,kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar jin dadin alhazan Alhaji Badaru Bello Karofi ya sanar daga can kasa mai tsarki. 

Post a Comment

Previous Post Next Post