Hajj 2024:AMIRUL HAJJ NA JAHAR KATSINA YA GANA DA MALAMAI A BIRNIN MAKKA BAYAN KAMMALA AIKIN HAJJI.

Hajj 2024:AMIRUL HAJJ NA JAHAR KATSINA YA GANA DA MALAMAI A BIRNIN MAKKA BAYAN KAMMALA AIKIN HAJJI. 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Amirul Hajj na jahar Katsina, tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Tukur Ahmad Jikamshi yayi taro da malaman da gwamnatin jahar ta dauki nauyin su zuwa aikin hajjin wannan shekara don taimakawa alhazan jahar  a wajen fadakarwa, ilmantarwa tare da wa'azantarwa akan yadda ake yin aikin hajji. Yin taron na da nufin yin bitar abubuwan da suka faru a lokacin gudanar da aikin tare kuma da abin da za'ayi bayan kammala aikin kamar yadda shi Amirul Hajjin ya nuna. 
Amirul Hajjin har ila yau, yayi kira ga malaman da su Æ™ara wayar da kan Alhazan ga batun komawa gida bayan kammala aikin Hajjin na su yi amfani da sauran kwanakin da ya rage masu wajen ci gaba da Addu'o'i,ga jaha da Kasar mu tare da shi kan shi Gwamnan kamar yadda ya roke su domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da karuwar tattalin arziki da nemawa Gwamnan karfin imanin da zai jagoranci jahar don aiwatar da adalci a tsakanin al'umma. Alhaji Tukur Jikamshi ya kuma kara yin kira ga Malaman da su fadakar da Alhazan akan yanayin zafi da ake ciki a kasar ta Saudiyya don kauce fuskantar wata matsala da zafin ka iya haddasawa,kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya baiyana acikin wata sanarwar manema labarai daga can kasa Mai tsarki. 
Shugaban Malaman da aka turan Shiekh Ibrahim Gora ya baiyana  jin dadin su da kuma godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Mallam Dikko Umar Radda phD da Tawagar Amirul Hajjin tare da shugabannin Gudanarwa da na Zartaswa na hukumar jin dadin alhazan ta jahar Katsina akan yadda aka zaÉ“o su domin bayar da gudunmawar su ga alhazan don su samu Hajj mabrur. Ya kuma baiyanawa Amirul Hajjin cewa kwamitin su na malamai masu Wa'azi ga Alhazai sun yi bakin Æ™oÆ™arin su na fadakar da Alhazan a dukkan wuraren da suka kamata don ganin sun yi aikin Hajjin acikin nasara. 
Shi kuwa Malam Shafiu Alkasim Saulawa a madadin sauran malaman, nuna godiyar su ga Gwamnan Mallam Dikko Umar Radda phD suka yi bisa ga ziyarar da ya kaima Alhazan Jihar Katsina a tantunan su Minna tare da zagayawa domin ganawa tare da ganin halin da alhazan suke ciki Wanda a cewar shi wannan ya nuna irin  Jagorancin da Gwamnan ke yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post