YADDA AKA GUDANAR DA ZABEN ƘUNGIYAR NURTW RESHEN TAKSI MAI DOGON ZANGO A KATSINA
A ranar asubucin nan 25 ga watan Mayu, 2024 aka gudanar da zaben sabbin shugabannin da zasu jagoranci kungiyar NURTW reshen taksi mai cin dogon zango dake babbar tashar Katsina, bayan cikar wa'adin shugabancin wadanda suke rike da ragamar mulkin ya kare wanda har saida aka sanya kwamitin riko wanda uwar kungiyar ta jaha ta kafa har na tsawon wasu watanni kamar yadda dokar ta bayar da damar yin hakan a inda aka gaza samun daidaito a tsakanin 'yan takara.
Shi dai wannan zabe na wannan yanki ana kallon shi da muhimmanci saboda wasu dalilai. Kadan daga cikin su shine, zamowar reshen acikin babban birnin jaha kuma acikin babbar tasha. Sannan za' a iya cewa reshe ne wanda ya haifar da wasu rassunan. Kazalika, duk wanda ke karkashin wannan reshe har batun zabe yazo, to mafi yawa suna da sha'awar aji sun fito takara.
A jawabin da ya yiwa 'yan takara da masu zaben, shugaban kwamitin yin zaben wanda kuma yake tsohon shugaban kungiyar ne a matakin jaha ya kuma rike shugabancin yankin arewa maso yamma na kungiyar, sannan daya daga cikin uwayen ƙungiyar a matakin kasa, Alhaji Yusuf Haruna ya ja hankakin 'yan takarar akan cewa, su sani shi fa zabe dole ne a ci kuma dole a fadi. To yana jan hankalin su da su rungumi kaddara ga wadanda suka fadi zaben. Su kuma wadanda suka ci, su sani ba dubarar su ba ce, sannan suyi adalci su rungumi kowa domin a gudu tare a tsira tare.
Kujeru biyar ne dai ake yin takarar su. Kujerar shugaba wadda mutane 3 suka fito nema, wato, Abdullahi Haruna, Abubakar Salisu da kuma Abdulkadir Abubakar. Amma daga baya shi Abdulkadir Abubakar ya janye takarar shi inda ya nemi magoya bayan shi da su zabi duk wanda suke ra'ayi.
Sai kujerar Sakatare wadda Isyaku Husaini da kuma Idris Salisu ke takara. Har'ila yau, kujerar Ma'aji na da mutane 2 dake so, wato, Basiru Sule da kuma Mannir Ilyasu. Ita kuwa ta Sakataren kudi mutane 3 ne suka fito. Abdullahi "What for you" da Muntari Isa da kuma Ma'aruf Sa'idu. Ita ma kujerar Mataimakin Sakatare ta samu jawara 2 masu son ta, wato, Bashir Sale(Asfa) da Halliru Isyaku.
Kazalika, kungiyar ta bi tsarin samun lamba ga dan takara domin samun saukin yin zabe. Ma'ana, an aza lambobi ga masu takarar wadda duk wanda ya dauka to wannan lamba za'a rubuta a wajen jefa mashi kuri'a. Sannan an rika kiran masu zaben ne daya bayan daya ana basu takardar jefa kuri'ar domin anyi zaben ne ta sirri.
Bayan kammala zaben, jami'in zaben wanda kuma shi ne Sakataren dake kula da shiyyar arewa maso yamma, Alhaji Yazeed ya baiyana sakamakon zaben inda a mukami Mataimakin Sakatare Basiru Sale yayi nasara da kuri'u 228 yayin da abokin karawar shi Halliru Isyaku yake da 104. Shi kuwa Abdullahi What for you ya samu kuri'a 250 inda ya zarce abokin takarar shi Muntari Isa mai kuri'a 902 a bisa kujerar Sakataren kudi. A mukamin Sakatare kuwa, Isyaku Husaini shi ke kuri'a 248 akan Idris Salisu mai kuri'a 89. Kujerar Ma'ajin kungiyar ta fada akan Basiru Sale da kuri'a 250 a inda abokin karawar shi Mannir Iliyasu mai. Ita kuwa kujerar shugaban kungiyar Abdullahi Haruna ne yayi nasara akan Abubakar Salisu da yawan kuri'u 252 akan 86. Sauran mukaman kungiyar an samu sasanci ne a tsakanin masu son kujerun.
Sakataren kungiyar na jaha Adamu Sabo ya rantsar da sabbin shugabannin. Membobi 378 ne suka jefa kuri'ar su a mukaman da aka yi takara akan su, cikin adadin yawan kuri'un da aka kada an samu wadanda suka lalace har guda 14.