SAUDIYYA TA BAYAR DA FILAYEN JIRGIN SAMA SHIDA DOMIN KARBAR ALHAZAN 2024.

SAUDIYYA TA BAYAR DA FILAYEN JIRGIN SAMA SHIDA DOMIN KARBAR ALHAZAN 2024.

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

 Kujeru miliyan 3.4 a cikin jirage 7,700 da aka ware domin gudanar da aikin hajjin bana na wata mai zuwa Mahajjatan Thai Umrah sun isa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah.
 Bugu da kari kuma, an kebe tashoshi 13 a filayen tashi da saukar jiragen sama guda shida da za su karbi maniyyatan da ma’aikata 21,000 za su yi aikin Hajji, kamar yadda kamfanin Matarat da ke kula da filayen jiragen saman Saudiyya ya bayyana.
 Kamar yadda kafar yada labarai ta Gulf ta ruwaito, Hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya sun ce sun kebe manyan filayen jiragen sama guda shida domin karbar musulmi, wadanda za su halarci aikin hajjin na daga wata mai zuwa.
Filayen su ne, filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah a tekun Bahar Maliya; Filin jirgin saman Yarima Mohammed bin Abdulaziz da ke Madina; Filin jirgin sama na Taif da ke yammacin birnin Taif; Filin jirgin sama na Sarki Khaled da ke Riyadh; Filin jirgin saman Yarima Abdulmohsen da ke birnin Yanbu da ke gabar teku; da filin jirgin sama na Sarki Fahd dake yammacin birnin Damam.

Post a Comment

Previous Post Next Post