KU YI HATTARA DA AMFANI DA KALAMAN KIYAYYA KO BATA SUNA A WAJEN RUBUTA RAHOTO - CDD ga 'yan jarida

KU YI HATTARA DA AMFANI DA KALAMAN KIYAYYA KO BATA SUNA A WAJEN RUBUTA RAHOTO - CDD ga 'yan jarida 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Anyi kira ga 'yan jaridu a jahar Katsina da su guji yin amfani da kalaman tozartawa ko ƙasƙantawa tare da kiyaye yin rahoton ɓata suna a yayin da suke rubuta labarai ko rahotanni musamman akan abin da ya shafi rashin jituwa ko wata babbar matsalar da take faruwa a tsakanin al'umma ba ma kamar abin da ya shafi tsaro.
Wannan kira ya fito daga É—aya daga cikin masu bayar da horo ga 'yan jaridun akan irin rawar da zasu taka a wajen rubuta rahotannin su akan rigingimu ko rashin jituwar da matsalar tsaron da 'yan bindigar daji masu garkuwa da mutane suka haddasa. Taron wanda cibiyar ci gaban Demokaradiya da ake kira "Centre for Democratic Development CDD ta shirya na tsawon kwanaki biyu domin ganin cewa an samu sahihan rahotannin da zasu kawo zaman lafiya.
Dokta Abba har ila yau, a wajen laccar da yayi a lokacin bayar da wannan horo, ya ja hankalin 'yan jaridar da su kiyaye kamalai ko rahotonnin da basu da cikakkiyar shaidar da zata kare su a gaban kotu yayin da aka shigar da ƙarar bata suna. "Kar ku rubuta labarin da wani zai baku ba tare da kun samu cikakkiyar sheda ba akan zargi ko furucin da yayi". A yanayi irin na tashin hankali ko shiga cikin wata damuwa, ku bayar da rahoton da zai kwantar da hankali koda acikin kawo hujja ko majiya mai karfi ce.
Shi dai wannan taron horassawa kungiyar na shiryawa 'yan jaridu ne domin kawo rahotannin sahihai musamman a yankunan da suke da matsalar tsaro, ba ma kamar ta 'yan bindigar daji. CDD na zaÉ“o 'yan jaridun daga kafofin yada labarai daban dabam dake cikin jahar ta Katsina. Ko a wannan karon,'yan jarida 20 ne suka samu wannan horo na kwanaki biyu da aka yi a Katsina. 

Post a Comment

Previous Post Next Post