Katsina PWB: AN GUDANAR DA TARON BAMBANCE TSAKANIN AYA DA TSUKUWA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
A cigaba da shirye-shiryen da take yi domin ganin anyi aikin Hajji na wannan shekara ta 2024 cikin nasara, an kira wani taron hadin guiwa a tsakanin É“angarori biyu na hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina, wato, bangaren gudanarwa da kuma na zartaswa a karkashin jagorancin Shugaban hukumar Alhaji Kabir Yusuf Bature Sarkin alhazai. Kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya baiyana a tsangayar shi dage a shafin Fesbuk, ya labarta cewa, taron wanda aka nemi Babban Jojin Jahar Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar da ya baiyanawa kowane sashe a tsakanin bangarorin biyu irin nauyi da kuma rawar da zai taka ko yake takawa a dokance.
Kamar yadda Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya ce a wajen bude taron bayan ya taya membobin gudanarwa na hukumar murna, ya ci gaba da cewa, "babban dalilin da yasa ganawa da shi Babban Jojin Jahar shi ne, domin fayyace aikin kowane sashe na hukumar kamar yadda doka ta tanada domin ganin cewa an samu nasarar gudanar da wannan aiki na bana cikin hadin kai tare da yin aiki kafaÉ—a da kafaÉ—a don a gudu tare a tsira tare.
A na shi ɓangaren wanda kuma yayi dogon bayani ga dukkan sassan biyu, Babban Jojin Mai Shari'a Musa Danladi yayi gamsasshen bayani akan kowane sashe da kuma irin rawar da zasu taka walau a tare ko daban-daban wanda a ƙarshe dai zasu hadu a wuri guda domin sabke nauyin da ya rataya akan su acikin wa'adin da doka ta ba su. Mai Shari'ar ya shawarci ɓangaren gudanar da cewa, su hada kai da sashen zartasawa a tsawon wa'adin da zasu yi na zama membobin wannan sashe na gudanarwa domin ganin cewa ana samun nasara a wajen tafiyar da aiyukan hukumar.
Shi kuwa shugaban hukumar Alhaji Kabir Yusuf Bature Sarkin Alhazai, nuna godiya da farin cikin su yayi ga shi Babban Jojin ta irin yadda ya warware masu zare da abawa akan aikin kowane sashe. Har'ila yau, ya kara jaddada kira ta su membobin gudanarwar hukumar akan su ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar domin ganin cewa an samu nasarar wannan aiki na Hajji na 2024 wanda shi ne aikin farko da zasu gudanar a matsayin su na membobin. Shugaban ya kara mika godiyar ga shi Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda ta irin yadda ya aza mashi nauyin shugaban wannan hukuma ta Alhazai, ya kuma tabbatarwa Gwamna cewar ba zasu bashi kunya ba a wajen aiwatar da aikin su.