JIHOHI FIYE DA 10 NE AKA KAIWA MANIYATAN SU BABBAR JIKKA BA KATSINA KADAI BA - Dan kwangila

JIHOHI FIYE DA 10 NE AKA KAIWA MANIYATAN SU BABBAR JIKKA BA KATSINA KADAI BA - Dan kwangila

Dangane da wasu ƙorafe-ƙorafe da suka taso akan baiwa maniyatan jahar Katsina babbar jikka maimakon kanana kamar yadda aka saba a shekarun baya wanda ake ganin kamar akwai wani shiri na daban akan haka da kuma ganin cewa, abin zai yiwa maniyatan wahala wajen daukar ta da kuma shiga jirgi.
Dan kwangilar da yayi aikin kawo wadannan jikkuna daga kasar China zuwa gida na Najeriya da kuma kasa mai tsarki, Alhaji Sulemain Yusuf Sulemain Jibiya ya baiyana cewa, ba jahar Katsina ba ne kadai aka kawo wadannan jikkuna, akwai wasu jihohin tare da baiyana dalilan da suka kawo faruwar haka.
"Farko dai jahar Katsina an bamu aikin kawo wadannan jikkuna ne a cikin kwanaki 8 a yau kuma muka yi kokarin kawo su domin gida ne. Sannan yana da kyau mutane su gane cewa, ita fa wannan jikka ta alhazai ba kamar yadda ake yi na sauran 'yan kasuwa ba ce. Ita jikka ce ta musamman".
"Sannan batun kawo manyan jikkunan. Jama'a su sani cewa, a halin yanzu akwai jihohi fiye da 10 da muka kaiwa wadannan jikkuna. Akwai jihohin Kano, Kebbi, Kwara, Bauchi, Filato, Sokoto, Taraba da Zamfara. Akwai ma sauran wasu jihohin da suke jira".
"Har ila yau, babbar matsalar da ta kawo wannan ita ce, batun yakin da ake yi a halin yanzu a Isra'ila. Sanin kowane cewa, dole ne sai jirgin daukar kayan nan ya biyo ta wannan yanki ko da kuwa na sama ne muddin zai fito da wannan yanki. To abin da ke faruwa shi ne, su 'yan tawayen nan babu ruwan su daga inda jirgi ya fito, suna iya kai mashi hari su tarwatsa shi a kowane lokaci".
Alhaji Sulemain ya ce, wannan ita ce babbar matsalar da ake fuskanta kuma ba wai maniyatan Najeriya kawai abin ya shafa ba. Daga nan sai ya tunasar da su cewa, wasu kasashen ma duk jikkunan biyu ake basu kafin su tashi zuwa kasar Saudiyya, misali, kasar Nijer. Sannan ya ce, mu anan Najeriya muna cikin wadanda ake yiwa gata na nauyin jikkar. 
Karshe yayi kira ga jama'a akan cewa, su rika bin diddikin faruwar abu kafin su bayar da labari akai. Sannan yayi godiya ga hukumomin alhazan da sauran masu ruwa da tsaki akan irin fahimta da kuma goyon bayan da suke bayarwa domin ganin aikin yayi nasara. Karshe ya mika godiya ta musamman ga gwamnatin Jahar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda da suka bayar da wannan aiki ga 'yan kwangila na jaha maimakon a dauko wani daga waje. 

Post a Comment

Previous Post Next Post