HUKUMAR KWASTAM TA SHA ALWASHI KAMAWA TARE DA GURFAR DA WADANDA SUKA KASHE JAMI'IN TA A GABAN KULIYA A KATSINA.

HUKUMAR KWASTAM TA SHA ALWASHI KAMAWA TARE DA GURFAR DA WADANDA SUKA KASHE JAMI'IN TA A GABAN KULIYA A KATSINA.

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Bashir Adewale Adeniyi, MFR, ya sha alwashin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka kashe jami'inta Mataimaki na ll, Auwal Haruna a Jihar Katsina. Hukumar ta Kwastam ta sha wannan alwashi ne a lokacin da ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin a garin Ƙayawa dake karamar hukumar Dutsi ta jihar Katsina. Hukumar ta karawa da cewa, ta na yin duk mai yiwuwa don kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
In za'a tuna an kashe Haruna ne a yayin wani mummunan hari da wasu da ake zargin ‘yan fasa kwauri ne suka kai wa jami’an Kwastam a shingen bincike na Gamjin Makaho da ke kan hanyar Katsina zuwa Dankama a karamar hukumar Kaita ta Jihar Katsina a ranar 17 ga Afrilu, 2024.
Kamar yadda Kakakin hukumar SC Tahir Balaraba ya shaida a sanarwa da fitar ga manema labarai ya ce, Babban Kwanturolan Adeniyi wanda ya samu wakilcin wata babbar tawaga karkashin jagorancin kwamandan hukumar kwastam ta jihar Katsina, Kwanturola Muhammad Umar, ya ce tuni hukumar kwastam ta fara gudanar da bincike kan lamarin kuma za ta zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
 Babban Kwanturolan na Kwastam ya sha alwashin cewa wadanda suka kashe jami’in Kwastam din da aka kashe za su fuskanci hukunci, ya kara da cewa kowane ma’aikacin sa na da muhimmanci, “don haka ba za mu taba barin wadanda suka aikata laifin a ‘yantar da su ba. Ya bayyana cewa NCS za ta tabbatar da kama wadanda ake zargin tare da hukunta su yadda ya kamata, yana mai cewa lamarin yana da zafi kuma ba za su taba mantawa da shi ba.
 Hukumar Kwastam wadda ta bayyana kisan jami’in nata a matsayin wanda bai dace ba, ta kuma nuna matukar bakin cikinta game da rasuwar jami’in tare da jajantawa iyalan marigayin da daukacin al’ummar Kayawa.
 Ya ce wannan danyen aikin da aka kai wa jami’an Kwastam ya nuna irin hatsarin da jami’an hukumar ke fuskanta a bakin aiki, tare da jinjina wa jarumtaka, jajircewa, kishin kasa da kishin aiki. Babban Kwanturola na kasa ya ce: “NCS tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen kamo wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da sun fuskanci fushin doka.
Adeniyi yayin da yake addu’ar Allah ya jikan Haruna, ya kuma tabbatar wa iyayensa da al’ummar Kayawa cewa hukumar kwastam ta Najeriya za ta ci gaba da kasancewa tare da su a lokacin jimami da kuma bayan zaman makoki. Ya kara da ce ofisan da aka kashe ya bi sahun manyan mutane wadanda suka ba da duk abin da suke da shi, tare da girmamawa, a hidimar kasarsu ta uwa da uba.
 A lokacin da mahaifin jami’in da ya rasu yake kokarin yin jawabi ga tawagar, sai da fara fashewa da kuka ba kakkautawa don haka ya kasa magana.
Shi kuwa Shugaban karamar hukumar Dutsi, Alhaji Ado Rabe, wanda ya yi magana a madadin ‘yan uwa ya roki mahukuntan hukumar ta NCS da su maye gurbin marigayi Haruna da daya daga cikin iyalansa. Ya ce daukacin al’umma sun yi rashin É—a wanda shi ne ma’aikacin kwastam daya tilo a yankin, don haka akwai bukatar hukumar kwastam ta Najeriya ta duba yiwuwar maye gurbinsa.
 A jawabin shi ga tawagar a gidan gwamnati dake Katsina, Gwamna Dikko Umaru Radda, ya bukaci jami’an tsaro a jihar da su kamo wadanda suka kashe jami’in kwastam din domin fuskantar shari'a 
 Ya ce: “Yana da matukar muhimmanci jami’an tsaro da ke da alhakin gudanar da bincike, don tabbatar da an kamo kuma an gurfanar da wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su.
 “A madadina da na al’ummar Jihar Katsina, na mika ta’aziyya ga Kwanturolan Janar na Kwastam, da daukacin ma’aikatan Hukumar bisa asarar da ba za a iya maye gurbinsu ba.”, inji Gwamna Radda. Ya ce, duk da haka, huldar da ke tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da al’ummomin kan iyaka a jihar na da kyau da kuma samun sakamako mai kyau, don haka akwai bukatar dorewar ta. Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin da Aljannar Firdaus “saboda ya rasu yana kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa”.
 Tawagar ta kuma ziyarci Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar, domin irin wannan ta'aziyya, inda ya yaba da kyawawan halayen marigayin. Sarkin ya bukaci hukumar kwastam ta Najeriya da ta jajirce wajen kwato hakki na hukumar, tare da magance fasakwauri da sauran laifukan kan iyaka a jihar.
 Tawagar Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta hada da Kwanturola Janar na shiyyar B, Kaduna, Ahmadu Bello Shu'aibu; Kodinata na hadin guiwa masu kula da kan iyaka É“angare na 4, Kwanturola Aminu Abubakar, da sauran manyan ofisoshin hukumar. 

 

1 Comments

  1. https://www.facebook.com/share/v/uBm12GF9xMPJJGL1/?mibextid=xfxF2i
    Above is my view on the behavior of Nigerian Custom.
    There are cases of Nigerian Custom killing civilians in Katsina and the cases were cuision down through dialogue
    So this case must be investigated but the Root cause need to be identify

    ReplyDelete
Previous Post Next Post