Hajj2024: MAHAJJATAN JAHAR KATSINA ZASU SHAIDA NAMAN HADAYAR DA GWAMNATI TA BIYA MASU - Dr. Ahmad

Hajj2024: MAHAJJATAN JAHAR KATSINA ZASU SHAIDA NAMAN HADAYAR DA GWAMNATI TA BIYA MASU - Dr. Ahmad 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Don ganin mahajjatan jahar Katsina basu shiga cikin matsatsi mai yawa akan sha'anin kudi a yayin da suke gudanar aiyukan Hajji na 2024 yasa gwamnatin Jahar karkashin jagoranci Gwamna Malam Umar Dikko Radda ya biyawa mahajjatan dubu biyu da dari bakwai da sittin(2760)kudin hadaya na Riyal 720 kudin Saudiyya wanda ya kasance sama da naira dubu dari. 
Babban shugaban hukumar Zakka da WaÆ™afi na jahar Katsina wanda kuma shi ne shugaban kwamitin hadayar Dokta Ahmad Musa Abdullahi ya shaidawa wakilin mu a yayin wata hira da suka yi da shi cewa, Gwwmna Radda ya dauki wannan mataki ne na biyawa mahajjatan wadannan makudan kudade bisa wasu dalilai guda uku. Daga cikin su akwai batun tausayawa mahajjatan bisa ga irin yanayin da suka biya kudin aikin Hajjin na bana da suka haura naira milyan takwas sannan kudin guzurin da aka basu na dalar Amurka dari hudu da 'yan kai zuwa dari biyar. Abu na biyu na dalilin Gwamnan shi ne, irin kura-kuran da ya gano an samu a lokuttan baya wadanda suka hada har da yaudarar mahajjatan ta amsar kudaden su da sunan za'ayi masu hadayar amma a karshe ba'a yi. "Dalili na uku na Maigirma Gwamna shi ne, fatan mahajjatan zasu yiwa jaha da kasa gami da al'ummar mu addu'o'in samun zaman lafiya da karuwar arziki. Wadannan sune manyan dalilan Gwamna na biyan wadannan kudade". 
"Wannan nauyi na yin wannan muhimmin aiki sai Allah ya aza nauyin gudanar da shi a karkashin hukumar Zakka da Wakafi sannan bisa jagoranci na a matsayin shugaban hukuma kuma shugaban kwamitin". 
Dokta ya tabbatarwa da mahajjatan cewa, wannan nauyi zasu yi kokarin sabke shi tare da abokan aikin da aka azawa wannan nauyi. 
"Ba wai su mahajjatan da muke tare da su ba, hatta sauran jama'ar jahar Katsina dake zaune a gida zasu san halin da ake ciki da zarar lokacin yin hadayar ya zo domin babu abin da zamu rage ko mu boye ba tare da sanin jama'a. Sannan akwai tsarin da muka yi inda kowane mahajjaci zai san an sayi dabbar da sunan shi, domin akwai rasidin da za'a ba shi kuma sannan zai ga sanarwa a wayar shi. Kazalika, a wajen yanka ma haka". 
To ko yaya mahajjacin zai shaida naman da aka yi mashi hadayar? Tambayar da muka yiwa shugaban kwwmitin kenan, inda yace, sun tanadi wadanda zasu soya naman domin baiwa mahajjatan su shaida. Sai dai yace, ba wai duka naman dabbar da aka yanka za'a baiwa mutun ba, za'a dai hada ko mutun biyar ko abin da ya sauwaka a soya masu rago guda, domin ai shi naman an san yadda addini ya shimfida ayi da shi. Sannan ita kanta hukumar Saudiyya mai kula da wannan sashe akwai irin nata tsarin yadda ake tafiyar da naman duk da aka yanka. 
Ƙarshe, Dokta Ahmad yayi kira ga mahajjatan kada su yarda da duk wanda yace su sake biyan wasu kudin hadayar domin ba'a yi masu ba. "Duk wanda ya zo yace a bashi kudi zaije ayi maka hadaya ka dauka mayaudari ne kawai, domin babu alhajin da aka bari baya. Sai dai ina kara mika godiyar mu ga shi Maigirma Gwamna a madadin duk wani alhajin jahar Katsina akan wannan kokari da kuma gudunmuwar da ya baiwa wannan aiki na hajji. Lallai ya nuna abin yana cikin jikin shi kuma yana fatan ganin cewa mahajjatan sun yi aiki karbabbe", inji shugaban kwamitin hadaya kuma Babban Shugaban hukumar Zakka da WaÆ™afi na jahar Katsina Dokta Ahmad Musa Abdullahi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post