Hajj2024: HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA ZA TA HADA HANNU DA SASHEN KIWON LAFIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Katsina za ta hada kai da masu aikin kula da kiwon lafiya wajen inganta tsafta da tsaftar muhalli musamman a lokacin aikin Hajji na wannan shekara ta 2024.
Shugaban tawagar kuma shugabar kungiyar ta jiha: ‘Yar uwa Halima Abubakar Danmune ta ce sun kasance a hukumar jin dadin alhazai ne domin neman karin tallafi kan ayyukan da suke yi a lokacin aikin Hajji. Halima Abubakar Danmune ta bayyana ayyuka daban-daban da ya kamata a kula da su kan harkokin kiwon lafiya domin inganta tsaftar muhalli da dakile yaduwar cututtuka daga wannan zuwa waccan.
A sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya bayar ya ce, a nashi jawabin, Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina Yunusa Abdullahi Dankama ya ba membobin kungiyar tabbacin ba su cikakken goyon baya kan gagarumin ci gaban da suke samu tare da yin alkawarin samar da duk wata damammaki da ake bukata wajen isar da ayyukansu.
Babban Daraktan ya bayyana haka a bayan karbar bakuncin ‘yan kungiyar a lokacin ziyarar ban girman da suka kai ofishin shi.
Shugaban ya ce mambobin kungiyar sun sadaukar da abin da suka samu a matakai daban-daban na manyan makarantun kiwon lafiya wajen taimaka wa alhazai na jihar Katsina da hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina.
Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya jaddada cewa sama da mahajjata dubu biyu da dari shida da sittin ne suka yi rajista domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024 zuwa yau: Dole ne a tabbatar da kokarin samar da matakan kariya domin kaucewa barkewar cututtuka da kuma inganta tsaftar muhalli.