Hajj 2024 : WAJIBI NE GA ALHAZAI SU KASANCE TARE DA KATIN SHEDAR SU – Saudi Arabia
Ma’aikatar aikin Hajji ta kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa a shafin ta na Twitter inda ta bukaci maniyyatan aikin Hajjin wannan shekara da su kasance kowane lokaci suna tare da katin shaidar su. Hukumar ta bayyana a shafinta na twitter cewa daukar katin shaida na alhazai yana taimakawa hukumomi ware maniyyatan da ba su yi rijista ba. Ta kuma ce katin yana sanar da mutane bayanai daban-daban da katin guda zai iya bayarwa: -
- Bayani kan shugabannin alhazai.
- Kamfanin dake da ke da alaƙa da su wajen hiidima
- Wurin zama a cikin Wuri Mai Tsarki
- Bayanan sirri na mahajjaci
Hukumar ta kara da cewa wannan kati wajibi ne kuma dole ne a rika daukarsa a duk tsawon lokacin aikin Hajji, daga zuwan alhazai har zuwa tashin su bayan gama aikin Hajjin. Don haka duk alhazai na duniya ana nasiha da su rike katin shaidar da ba za a iya canjawa ba.