Hajj 2024: AN KAFA KWAMITOCIN DA ZASU TAIMAKAWA MANIYATAN JAHAR KATSINA

Hajj 2024: AN KAFA KWAMITOCIN DA ZASU TAIMAKAWA MANIYATAN JAHAR KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka

A ci gaban shirye-shiryen da take na ganin cewa maniyatan jahar sun gudanar da aikin Hajji cikin natsuwa da kwanciyar hankali tare da sa ran samun karbabben aikin, hukumar jin dadin Alhazai ta jahar karkashin jagorancin Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ta kafa wasu kwamitoci da zasu gudanar da aiyuka a bangarori daban daban da suka shafi aikin tun daga nan gida har zuwa kasa mai tsarki.
Sanarwar kafa kwamitocin da fito daga bakin Daraktan tsara gudanar da aikin Alhaji Yusuf a wajen taron ganawa da Amirul Hajj Tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi ya kirawo dukkan sassan jami'an da zasu gudanar da aiyuka tun daga na kananan hukumomi har zuwa na jaha. Jami'an da aka kira taron ganawar domin su sun hada da masu wa'azi, jagororin alhazai, jami'an kiwon lafiya, masu nunawa alhazai hanya da kuma masu kula da lodin kaya da sauran su. Har'ila yau, kadan daga cikin kwamitocin sun hada da masu kula da raba abinci, tsabta, zirga-zirga da ta hada har da kai ziyara, kula da kaya da sauran aiyuka a can kasa mai tsarki a yayin da ake gudanar da aiyukan na Hajj.

Tun farko sai da Babban Daraktan ya shaidawa mahalarta taron irin shirye-shiryen da hukumar take ta yi babu dare ba rana da kuma irin gudunmuwar da gwamnatin Jahar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda ke baiwa hukumar don ganin an samu gudanar da aikin acikin nasara.
Shi kuwa shugaban taron, wato, Amirul Hajj Alhaji Tukur Jikamshi wanda Mai Shari'a Abbas Bawale ya wakilta ya ce, wadanda aka zabo domin yin wannan aiki su sani wata rahama ce daga Allah. Sannan ya ja hankalin su akan cewa, kowa yayi aiki a bisa inda ya ga an sanya shi yin aikin kuma ya rike shi da muhimmanci. Sannan yayi kira ga jami'an kiwon lafiya da su yi aikin su bakin iyawar su. Ya kara da cewa, duk wani wanda aka dorawa wani aiki to ya sani za'a sa ido domin ganin yayi shi daidai kuma za'a rubuta rahoto akan duk wani wanda aka azawa wani nauyi akan irin yadda ya sabke shi. Amirul Hajjin ya ci gaba da cewa, lallai ne a zamo masu biyayya a tsakanin juna sannan a tsare doka.
Shi kuwa shugaban hukumar jin dadin alhazan Alhaji Kabir Bature wanda shi ma ya samu wakilcin Alhaji Aliyu Radda ya ja hankali ne akan wasu abubuwa guda uku. Abu na farko shi ne, jajircewa ga aikin domin ganin anyi nasara. Sai kuma yin hakuri, domin shi aikin na Hajj gaba dayan shi hakuri ne. Kada a zamo masu saurin fushi akan tambaya ko wani abin da maniyaci ya nema. Sai abu na uku shi ne, jin tsoron Allah. Kada wanda aka azawa wani nauyi ya dauka ya fi kowa ko zai iya yin wani abin da yake ganin dubara ce ko son zuciya. Idan babu tsoron Allah a cikin kowane lamari to mutun ya sani bashi da wata riba, musamman shi wannan aiki na Hajji wanda ya fito da tsoron Allah a fili, inji Shugaban hukumar jin dadin alhazan Alhaji Kabir Bature sarkin Alhazai ta bakin Malam Aliyu Radda. 

Post a Comment

Previous Post Next Post