GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA BIYA WA MANIYATAN JAHAR SAMA DA DUBU 2 KUDIN HADAYA NA RIYAL 750 GA KOWANE MANIYACI

GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA BIYA WA MANIYATAN JAHAR SAMA DA DUBU 2 KUDIN HADAYA NA RIYAL 750 GA KOWANE MANIYACI

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A taron kaddamar da kwamitin wakilan da zasu wakilci gwamnatin Jahar Katsina a wajen aikin Hajjin wannan shekara ta 2024, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya shaida cewa, ganin irin namijin kokarin da maniyatan jahar suka yi na biyan kudin kujerar da ya haurawa milyan takwas hakan yasa ita kuma gwamnatin ta daukewa maniyatan kudin hadaya na riyal 720 kwatankwacin naira dubu 90 da wani abu(yana iya hawa ko sabka) kamar yadda kasar Saudiya ta sanar. Har'ila yau, Gwamnan yace, bisa ga irin wadannan kokari ne yasa duk wani abin da hukumar jin dadin alhazan ta kawo mashi yake yin sauran amincewa domin kada a samu wata tangarda a wajen gudanar da aikin.
Gwamna Radda ya kara da cewa, akwai babban aiki ga su wannan kwamiti wanda yake fatan zasu yi kokarin sabke wannan nauyi. "Ina so ku sanya ido sosai akan yadda ake gudanar da aikin daga kowane sashe sannan ku kawo rahoton irin yadda aikin ya gudana ba tare da tsoro ko jin kunya ko shakku ga duk inda kuka ga anyi ba daidai ba. Lallai a kula da batun masabkai da bayar da abinci tare da zirga-zirga da sauran duk wasu aiyuka. Sannan ina so ku sani, baya ga wadancan kudin hadaya, akwai kuma goron salla da zai biyo baya in Allah ya so. Fatan mu dai shi ne Allah yasa ayi aikin cikin nasara kuma karbabbe".
Shi dai kwamitin mai membobi 11 karkashin shugabancin tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Tukur Jikamshi sai Alh.Abubakar Abdulmumini Kabir Hakimin Jikanshi daga masarautar Katsina, Mai Shari'a Bawale Abashe, Umma Tukur, Safiyanu Yusuf Dansanwai daga masarautar Daura, Zaiyan Abba, Aliyu Mustapha Dankama. Sauran su ne, Sani Ali Ahmed, Shiekh Ahmed Filin Samji, Musdaha Liman Ratibi Sai Wakili daga ofishin Gwamna a matsayin Sakatare.
Da yake jawabi a madadin membobin kwamitin, shugaban kwamitin bayan yayi godiya sannan ya jinjinawa Gwamnan akan irin yadda ya zakulo mutane daga kowane sashe cikin kwamitin. Sannan ya tabbatarwa Gwwmna cewa, zasu yi aiki tsakanin su da Allah ba kuma zasu ci amanar Gwamnan ba. Sannan ya tabbatarwa Gwamna cewa, shi da kan shi zai mikawa Gwamnan cikakken rahoton da suka tattara wanda kuma ba zasu nuna son zuciya a wajen rubutawa tare da mikawa ga gwamnatin domin sanin abin yi a gaba. 

1 Comments

  1. To Allah yasa zaa yanka.
    Inaga kamata yayi
    1. Ai kwamiti goma na mutun Ukku Ukku. Wakillan Gwamnati 2 Mai wakiltar Alhazai Daya.
    2. Tunda Alhazai 2000 ne ko wane kwamiti a basu Alhakin Alhazai 200.
    3. Kowane kwamiti zaa tabbatar da yasayi Dabba 200.
    4. Idan anzo yanka . Kowane kwamiti zaizo da list na Alhazan da ya saima dabbobi.
    5. Kafin a yanka Dabba sai angayama Mai yanka sunan Alhajin Dake da Hadayar sannan ya yanka.
    6. Akwai zama da. Zaai na tantamce Yan kwamiti a gaya masu kaidojin aikin su.
    7. Kowane kwamiti zai raba Alhazan shi Maza da Mata Kuma bayan yanka zaa fidda ma Maza da Mata Naman su . Misali Mata Goma a basu Rago Guda.
    8. Maganar Kudin soyen Nama Gwamnati zata dauka.
    9. Kenan zaa soya Rago 200 . Kenan Tukari mazauna Garin Makka zasu samu Aikin Soya Nama karkashin Jagorancin Gwamnatin Katsina.
    10. Karshen Hidima duka Kwamitocin zasu hada Rahoton Yadda sukai ayyukan su. Nasarori da Matsaloli da Shawarwari.
    Wannan shine Shawara ta. Gudun Kar a samu Korafi ko Matsala.
    Nagode
    Ibrahim Sogiji Katsina

    ReplyDelete
Previous Post Next Post