GWAMNA RADDA YA ROƘI HUKUMAR SAMAR DA ABINCI TA DUNIYA DA A GAGGAUT KAWO KARSHEN MATSALAR TSARO AREWA

GWAMNA RADDA YA ROƘI HUKUMAR SAMAR DA ABINCI TA DUNIYA DA A GAGGAUT KAWO KARSHEN MATSALAR TSARO AREWA 
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya roki Hukumar samar da abinci ta Duniya (WFP) ta dauki matakin gaggawa a daidai lokacin da ake fama da rikicin Arewa maso Yammacin Najeriya
 Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bukaci a gaggauta kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin na Arewa maso yammacin Najeriya.
 Da yake magana a wani taro da aka yi kwanan nan a Abuja tsakanin jami’an gwamnatin jihar Katsina da wakilai daga hukumar samar da abinci ta duniya (WFP), Malam Radda ya yi karin haske kan munin rikicin.
 Kamar yadda Babban Sakataren Labarai na Gwamnan Malam Ibrahim Kaula Mohammed ya baiyana a wata sanarwar manema labarai da ya fitar ya ce, yayin da Gwamna Radda yake bayyana wannan mummunan halin da ake ciki, a hannu guda Gwamnan ya godewa wakilan hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) karkashin jagorancin daraktan kasa David Stevenson, saboda amincewa da yankin Arewa maso Yamma a matsayin wani yanki mai mahimmanci da ke bukatar taimako.
 “Muna godiya ga Hukumar Abinci ta Duniya saboda amincewa da matsanancin kalubalen da muke fuskanta a Arewa maso Yamma. Shi dai wannan rikicin ya fara tasowa daga Arewa maso Gabas, inda ayyukan Boko Haram ya ya so zuwa Arewa maso Yamma, yanzu muna kan gaba a wannan yanki na yaki", inji Gwamna Radda. 
 Har'ila yau, Gwamnan ya ce tun lokacin da gwamnatinsa ta hau karagar mulki kusan shekara guda da ta wuce, ta kaddamar da ayyuka da dama na yaki da rashin tsaro, amma lamarin na ci gaba da ruruwa. Ya yi nuni da mummunan tasirin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a jihohin Zamfara da ake makwabtaka da su. A yayin da yake bayyana halin da jihohin biyu ke ciki a matsayin "mai ban tsoro", ya jaddada bukatar samun goyon bayan kasa da kasa cikin gaggawa.  
"Muna godiya da cewa shirin samar da abinci na duniya ya mayar da hankalinsa ga yankin Arewa maso Yamma. Yayin da wannan shiga tsakani ya zo a cikin wani mawuyacin lokaci,amma ba'a makara ba. Muna matukar bukatar taimako don magance wadannan kalubale," in ji Radda.
 Yayin da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa al’ummar jihar, Gwamna Radda ya bayyana matakan da suka dauka domin dakile illolin karancin abinci a jihar.
 “A cikin azumin watan Ramadan da ya gabata mun samar da dafaffen abinci ga mutane 72,000 a kowace rana na tsawon kwanaki 30. Bugu da kari, mun raba kayan abinci na Naira biliyan 10 tare da hadin gwiwar kananan hukumomi, inda muka sayar da su a kan farashi mai sauki don taimakawa gajiyayyu acikin al'umma, "in ji Radda.
 Gwamnan Katsina ya kuma bayyana cewa kimanin mutane 43,000 marasa galihu da suka hada da nakasassu da zawarawa da marayu suka amfana da tallafin kayan abinci da na kudi; kowanne daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin ya karbi buhun shinkafa da naira 10,000.
 Gwamna Radda ya kara bayyana kokarin gwamnatinsa na yaki da rashin tsaro ta hanyar samar da ayyukan yi. “A jiya mun kaddamar da wani shiri na horas da matasa maza da mata 3,000 a kan aikin injiniyoyi, inda za su ba da alawus a lokacin horon da suke na watanni shida,” in ji shi. “Mun ware naira biliyan 3.4 ta hannun hukumar bunkasa sana’o’i ta jihar Katsina tare da hadin gwiwar bankin Amana Micro Finance domin tallafa wa wadannan da suka samu horon wajen samar da bita da daukar wasu ma’aikata.
 Har ila yau, a fannin noma, Gwamnan Katsina ya bayyana cewa gwamnatinsa na kokarin bunkasa noma ta hanyar samar da ingantattun iri, ingantattun ayyuka, da abubuwan da suka dace ga kananan manoma.
  "Mun samar da Cibiyar Injiniyoyi don samar da kayan aikin noma na zamani akan farashi mai rahusa "A wannan makon mun shirya raba buhunan taki guda 400,000 wanda kudinsu ya kai Naira biliyan 22 ga manoma."
 Gwamna Radda ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na yin hadin gwiwa. 
 "A shirye muke mu hada kai da kuma daidaita kayan aiki tare da ku don cimma burinmu na bai daya," in ji shi

Post a Comment

Previous Post Next Post