Cika shekara guda a ofis: GWAMNA RADDA GWARZON ZAMANI - Ashiru Tankuri
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
"Idan alheri ne kuma zan yi adalci in taimaki al'umma nike neman wannan kujera Allah ka bani, in kuma ba alheri zan zamowa al'ummar jahar Katsina, Allah ka baiwa wanda ya fi"
Kowane lokaci irin kalaman da Alhaji Ashiru Tankuri ke tunawa da su kenan a lokacin da Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya rika fadawa jama'a a duk inda yaje yakin neman zabe a 2023. To ashe alherin ne ga jama'ar jahar Katsina domin Allah ya amshi wannan addu'a ta shi domin da gaske yake yi bada nufin zalunci ko yaudarar al'umma.
Alhaji Ashiru Tankuri na daya daga cikin manyan 'yan kasuwar dake sayar da kayan masarufia jahar Katsina wanda kuma al'umma ke yaba irin yadda yake tafiyar da harkokin kasuwanci na rashin tsauwalawa jama'a domin cin kazamar riba. A hirar da wakilin mu yayi da shi, Alhaji Tankuri yace, "mu a yanzu babu abin da zamu ce ga shugabancin wannan bawan Allah illa ci gaba da yi mashi addu'o'in samun nasara akan irin aiyukan da yake kokarin yi da kuma wadanda yake cikin yi domin ci gaban al'ummar jahar har ma da makwabta. Bari in kara maka bayani akan abin da kowa ya sani kuma ake gani a aikace ba labari ba. Ka ga maganar sha'anin tsaron nan, ba karamin aiki ba ne. Ni yanzu na fito daga Tankuri wanda kowa yasan irin yadda wadannan lunguna namu suka zamo lahira kusa ko kudin fansa. Dole ta sanya muka bar zuwa garuruwan mu saboda tsoro, amma yau mutun yana iya bin wannan hanya ta Batsari ka yanke ka shiga Tankuri ka wuce Gangara har ka fita zuwa Jibiya cikin aminci ba tare da zullumi ba, sabanin lokuttan baya".
Har'ila yau, irin hikimar da yayi ta daukar wadannan jami'an wadanda suka fito daga yankunan da ake fama da wannan matsala ba karamar hikima ba ce. Su suka san lungu da sako tare da sanin duk wani mugun dake yankin". Alhaji Ashiru ya ce, ko a fagen daga aka samu kwamandan yakin da ya shirya irin wannan dabara ya cancanci yabo koda a hannun makiya ne.
Da ya juya akan wasu batutuwan Alhaji Ashiru ya dubi batun harkar ilmi inda ya jinjinawa Gwamna Radda. "A lokaci guda ace an dauki malaman makaranta sama da dubu 7 abinda ba'a taɓa yi ba a tarihi ba wai a Katsina ba kusan a arewa baki ɗaya. Ga batun gyaran makarantun da kuma kokarin ganin an bar samun yaran da basu zuwa makaranta". Ɗan kasuwar har ila yau, yayi tsokaci akan irin yadda gwamnatin Dikkon ta baiwa masu rauni tallafin abinci da kudin cefane wanda yace Gwamnan ne da kan shi ya rika bayarwa, sannan ga batun ciyarwa a lokacin azumi.
"Wato in za'a ce zamu tsaya fadin abubuwan alherin da Gwamna yayi zamu dauki lokaci sai dai mu fadi kadan. Yanzu ko wannan aikin hanyar da ta tashi daga kofar Soro zuwa kofar guga ba karamin lamari ba ne musamman na ganin cewa, ba shi ne wanda ya kawo aikin ba da farko, amma ya tsaya yayi wanda hakan ya nuna cewa yana kokarin ganin ya aiwatar da duk wani aikin da ya gada daga gwamnatin baya, inda yake yin ƙari ga wasu, misali titin da ya nufo kofar gidan Ciroma. Batun fita waje da wasu ke magana, ni a nawa tunanin duk wani shugaba mai son cigaban al'ummar shi, to shi ke zuwa ya nemo ba wai ya tsaya abin ya same shi ba, haka nike ganin Gwamnan ke yi. Ya bi da kan shi. Sannan ga wani babban al'amari. Ka ga biyawa alhazai kudin hadaya da yayi? Gaskiya wannan abin ba karamin tasiri yayi ba. Ina da yakinin cewa, babu wani alhajin da ba zai yiwa jaha addu'ar fatan alheri da zaman lafiya tare da karuwar arziki ba, ba wai ga shi Gwamnan ba kawai. Wato ina so ka sani kai wannan ɗan jarida, da muna samun shugabanni masu kyakkyan kuduri ga wadanda suke yiwa shugabanci kamar yadda Gwamna Radda ke yi, da tuni kasar mu musamman arewa, da tuni mun wuce yadda muke a yanzu".
To ko Alhaji Tankuri yana da wata shawarar da yake ganin ya kamata a bi? Yace, tabbas akwai, "farko dai jin tsoron Allah da rike amana da kuma yin gaskiya. Sannan kasan duk inda shugaba yake sai an samu wannan sashe biyu, masu bashi shawara ta gaskiya da kuma masu yi don wata biyan bukatar su. To ina bashi shawara da ya rika kokarin bambance irin wadannan mutane. Sannan ya ci gaba da yin wannan salon mulki mai kama da irin na marigayi Umaru Musa yayi, Allah ne zai shige mashi gaba", inji, Alhaji Ashiru Tankuri