Katsina PWB - Ga maniyatan Hajj 2024: INDAN BABU FASFO BA BIZA BA TAFIYA HAJJI KODA AN BIYA KUDIN - Babban Darakta

Katsina PWB - Ga maniyatan Hajj 2024: INDAN BABU FASFO BA BIZA BA TAFIYA HAJJI KODA AN BIYA KUDIN - Babban Darakta

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Babban Daraktan hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama yayi kira ga maniyatan wannan jaha akan batun kawo fasfo na su don yi masu biza don tafiya aikin Hajjin wannan shekara wanda hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen yi. Daraktan ya ce, "ko da mutun ya biya kudin shi cif-cif acikin lokacin da aka kaiyade amma bai kawo fasfo na shi ba, ya sani cewar har in wa'adin da aka baiyana na rufe yin wannan biza ya cika, to lallai wannan babu shi babu zuwa wannan aiki domin sai da bizar kasar Saudiyya zata bari a shiga".
"Yanzu haka akwai wadanda suka biya kudaden na su amma har zuwa yanzun basu kawo fasfo nasu ba don yi masu bizar, wanda muke kira gare su da suyi hanzarin yin hakan domin bai wuce kwanaki biyu ƙasar ta Saudiya ta rufe hanyar yin bizar".
Alhaji Yunusa Dankama yayi wannan bayani ne ga maniyatan dake ci gaba da yin bitar su daga shiyyar Katsina a wannan rana ta litinin a hedkwatar hukumar. Babban Daraktan wanda ya kara jaddada irin mataki da shirye-shiryen da ita kasar ta Saudiyya ta dauka a wannan lokacin wanda ya sha bamban da na lokuttan baya, yace, dukkan wata ka'ida ko wani wa'adin da kasar ta bayar babu batun canzawa. A karshe Babban Daraktan yayi fata tare da addu'ar cewa, wannan bita da ake yi maniyatan na amfana da ita kuma zasu yi aiki da abin da suka ji ko suka koya. 
In za'a tuna, kasar ta Saudiyya ta baiyana cewar zata kammala duk wasu shirye-shiryen aikin Hajjin wannan shekara kwanaki hamsin kafin ranar Arafat domin ganin ta shawo kan duk wata matsalar da ka iya kunno kai. 

Post a Comment

Previous Post Next Post