Hajj2024: KUDIN GUZURIN MANIYATAN AIKIN HAJJIN BANA YA FADO KASA ZUWA DALA 500

Hajj2024: KUDIN GUZURIN MANIYATAN AIKIN HAJJIN BANA YA FADO KASA ZUWA DALA 500

Kamar yadda kafar yada labaran aiyukan Hajji mai zaman kanta,wato, "Hajj Reporters" ta sanar a shafin ta na yanar gizo, dukkanin maniyyatan aikin hajjin bana da suka biya kudin su ta jahohi 36 da sojoji za su samu kudin guzurin su (Basic Travel Allowance (BTA) na dalar Amurka 500 a wannan shekara. 
 An samu fargaba a tsakanin alhazai bayan da hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da fara jigilar maniyyata aikin hajjin ba tare da sanar da BTA da aka saba sanyawa cikin kudin a can baya ba lokacin da aka sanar da jimlar kudin aikin. 
 Masu aika rahotanni na ita wannan kafa mai zaman kanta sun sha yin kira ga hukumar da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su sanar da kudin guzurin BTA kafin lokacin don baiwa mahajjatan damar yin isassun tsare-tsare na tafiyarsu.
 Wata majiya mai karfi ta sanar cewa Hukumar ta sanar da Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihohi cewa maniyyatan da suka biya Naira miliyan 6.617 ko kuma milyan 8.254 a yankin Arewa da kuma Naira miliyan 8.454 a matsayin kudin aikin Hajjin daga shiyyar kudu za a ba su dala 500 na guzurin. 
 “Eh, NAHCON ta sanar da jihohi cewa BTA na bana dala 500 ne sannan an umarci mu gayawa maniyyatan mu hakan. Shugaban da kansa ne ya sanar da mu wannan bayanin, ina tsammanin kwanaki 2 ko 3 bayan masu aiko da rahotannin aikin Hajji masu zaman kansu sun fitar da sanarwar. Duk da cewa mun rigaya mun sani domin abu na 26 da gwamnati ta umarce mu a bayanan aikin hajjin da aka aiko mana a lokacin da aka tantance kudin da ya kai Naira miliyan 4.7 ya nuna cewa an ware Naira 425,000 ne a BTA kuma idan aka canza wadannan kudi zasu kama dala 500"in ji majiyar. 
In za'a tuna, ana biyan maniyyatan jihohi dala 800 a matsayin kudin guzurin na BTA tun a shekarar 2016 har zuwa lokacin da hukumar NAHCON ta karshe karkashin shugabancin Zilkifilu ta rage zuwa dala 700 a shekarar 2023 bisa wasu dalilan da ta baiyana da suka hada da batun tsadar man jirgi da kuma zagayewar kasar Sudan da za'a yi bisa dalilan fadan cikin gida da kasar ke fama da shi. 
 Su dai wadannan kudin guzuri suna cikin kuÉ—in aikin hajjin da maniyatan suka biya don basu damar samun kuÉ—in waje a Saudi Arabiya ta yadda zasu biya bukatun kansu yayin aikin hajji. Har zuwa rubuta wannan rahoto, bamu samu cikakken bayanin dalilin rage wadannan kudaden guzurin zuwa dala 500 daga ita hukumar aiyukan Hajji ta Æ™asa NAHCON ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post