Hajj 2024 : ZA'A INGANTA AIKIN JIGILAR ALHAZAI A FILIN JIRGIN SAMA NA KATSINA - FAAN
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
"...bayan aikin Hajji na 2023 da ya gabata, an samu kura-kurai da yawa wanda mahukuntan filin jirgin sama na suka lura da su"
An kafa kwamiti wanda Manajan filin jirgin na Umaru Musa Yar’adua a karkashin hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ya kafa domin ziyartar hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina akan batun gudanar da ayyukan Hajji na 2024 wanda zai gudana nan ba da dadewa ba.
A cewar shugaban kwamatin wanda kuma shi ne shugaban aiyuka na hukumar Jabir Mannir ya ce makasudin ziyarar sun ta’allaka ne da nazari bayan gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 da ya gabata, "akwai kurakurai da dama da suka samu a filin jirgin wanda mahukuntan filin suka lura da su, dalilin da ya sa manajan filin jirgin ya yanke shawarar kafa kwamitin a matsayin wani mataki na daukar matakai kafin a fara aikin Hajjin na bana.
Hukumar ta yaba wa hukumar jin dadin alhazai ta jiha bisa namijin kokarin da ta yi na gudanar da aikin Hajjin da ya gabata cikin nasara inda ta kara da cewa irin yadda hukumar jin dadin alhazan ta gudanar da aiyukan ta a bara abin yabawa ne.
Wakilin mahukuntan filin jirgin saman ya ci gaba da cewa akwai matsaloli da dama musamman ma dangane da ayyukan Hajji don haka hannu daya ba zai iya daukar aikin ba don haka ya kamata su hada kai don ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin na 2024.
A nasa martanin a madadin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina babban daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya bayyana jin dadinsa da ziyarar da suka kawo daga filin jirgin sama na FAAN Katsina tare da yabawa hukumar bisa kafa wannan kwamiti.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi, Dankama ya bada tabbacin ga hukumar kula da filayen jiragen sama na Katsina cewar a shirye hukumar da yake yiwa jagoranci ta ke don bada hadin kai da goyon baya domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara. Ya kuma shaida wa kwamitin cewa hukumar ta samu kimanin kujerun aikin Hajji 4,500 daga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a bana kuma ta sami damar yin rijistar maniyyata sama da 2,600 daga jihar.
Babban daraktan ya kuma shaida masu cewa, a wani bangare na shirye-shiryen atisayen, hukumar ta riga ta samu masaukin alhazai, da masu kula da abinci da sauran ayyukan Hajji ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Dangane da batun biza, Babban Daraktan ya ce hukumar ta samar da kusan kashi 50 na bizar da ake bayarwa a tsakanin sauran shirye-shiryen aikin
Daga cikin wadanda suka yi jawabi a lokacin ziyarar akwai shugaban hukumar Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai wanda ya nuna jin dadinsa ga hukumar kula da filayen jiragen saman da suka kafa wannan kwamitin tare da ba su tabbacin cewa hukumar za ta ba su dukkan goyon baya da hadin kai a wannan aikin Hajji na 2024.